✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu dakon man fetur sun ƙara farashi

Ana fargabar yiwuwar karin farashin man fetur a Najeriya bayan manyan masu dafo-dafon mai sun yi wa manyan dilllalai karin kudi

Ana fargabar yiwuwar karin farashin man fetur a Najeriya bayan manyan masu dafo-dafon mai sun kara wa dillalai farashi.

A ranar Litinin ne masu dafo-dafo suka kara kudi bayan farashin gangar danyen mai sanfurin Brent ya karu zuwa Dala $79.76 a kasuwar duniya.

Masu dafo-dafo irin su Swift, Wosbab, Sahara, da Shellplux, sun mayar farashin litarsu tsakanin N950 da N960, Naira N907 zuwa N912 da suke sayarwa a makon jiya.

Haka kuma an samu karin farashin litar man dizel a wurin Matrix Warri da Nipco ya karu da N72 zuwa N100 .

Dafon Stockgap sun kara kudin dako daga N1,080 zuwa N1,150, Ibeto sun kara daga N1,050 zwua N1,150 a kan kowace lita.

Bayanai sun suna farashin man N887.51 ne zuwa ranar 19 ga watan Disamban 2024, amma halin da ake ciki na nufin yiwuwar karuwar kudin nan gaba.

Hakan na zuwa ne bayan a ’yan makonnin da suka gabata aka samu raguwar farashin man a Najeriya zuwa tsakanin N935 da N965 daga N1040 da yake a baya, inda yanzu farashin yake tsakanin N935 zuwa N1,100 a kowace lita.