✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masu coronavirus a Kano sun haura 1,000

Kawo yanzu mutum 1,004 ne suka kamu da cutar coronavirus tun farkon bullar annobar a jihar Kano. Mutum 8,400 ke killace da cutar a fadin…

Kawo yanzu mutum 1,004 ne suka kamu da cutar coronavirus tun farkon bullar annobar a jihar Kano.

Mutum 8,400 ke killace da cutar a fadin Najeriya a halin yanzu.

Alkaluman Kano sun haura 1,000 ne bayan wasu mutum 5 a jihar sun harbu da cutar daga cikin mutum 315 da suka kamu a jihohi 14 a ranar Litinin.

Mutum 478 na kwance da cutar a jihar Kano, wasu 477 sun warke, 49 kuma ta yi ajalinsu, zuwa daren Litinin.

Kano ce jiha mafi yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya, bayan jihar Legas mai mutum 5,895.

A ranar Litinin masu cutar a Najeriya suka kai mutum 12,801, cikinsu 4,040 sun warke, 8,400 kuma suna killace.

Hukumar NCDC mai yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta kuma ce mutum 361 sun mutu daga cikin masu cutar da ta yadu zuwa jihohi 35 da kuma Birinin Tarayya a Najeriya.