✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu Albashin 7,000 A Borno Ta Bayan Fage Suka Sami Aiki

Shugaban Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) reshen Borno, Kwamred Garba Zali, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake biyan wasu malamai albashin N7,000 a jihar. Ya…

Shugaban Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) reshen Borno, Kwamred Garba Zali, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake biyan wasu malamai albashin N7,000 a jihar.

Ya ce, malaman da shafa sun tsinci kansu a wannan yanayi ne saboda hanyar batan fage suka bi wajen samun aikin karantawa a makarantun gwamnatin jihar.

Shugaban na NUT ya yi zargin cewa ba a bi tsarin da ya dace ba wajen daukar ma’aikatan da abin ya shafa.

Zali ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da horar da malamai 781 daga kananan hukumomi 19, a Kwalejin Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Umar Ibn Ibrahim Elkanemi da ke Bama.

Ya ce masu daukar irin wannan albashin sun sami aikin ba ta hanyar da ta dace ba.

A cewarsa, wasu sun sami aikin ne ta hanyar  cike gurbin malaman da suka yi ritaya da wasu da dama da aka dauka aiki ba tare da bin ka’ida ba.

Kwamared Zali, ya jaddada bukatar yi wa ɓanagaren ilimi gyara fuska a jihar Borno, musamman ma a matakin firamare.

Mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ya jaddada aniyar gwamnatinsu wurin inganta malaman makarantu.

Ya ambaci yadda ake ware kudade domin shirya tarukan horarwa da kuma tsare-tsaren mayar da malaman da basu cancanci karantawa ba waɗansu ma’aikatun.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha, da kuma Ƙirƙira, Injiniya Lawan Wakilbe, ya bayyana cewa za a sake fasalin tsarin karantawa da kuma tantance ma’aikata, da kuma tsarin ƙarin ilimi da shirye-shiryen ci gaba ga malamai.