✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa na neman N30m kan yara 3 a Kaduna

’Yan bindiga na neman miyagun kwayoyi da kayan abinci da kudi Naira miliyan 30 kafin su sako yara uku ’yan gida daya da suka sace…

’Yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu yara uku a Jihar Kaduna na neman kudin fansa Naira miliyan 30.

A makon jiya ne ’yan bindiga suka kutsa gidan wani likita suka yi awon gaba da ’ya’yansa uku a unguwar Azala da ke yankin  Katari a Karamar Hukumar Kachia.

Wani makusancin iyalan likitan mai suna Barnabas, ya ce, “Iyalan sun shiga tashin hankali saboda rashin samun tuntuba daga masu garkuwar.

“Sai a ranar Asabar da misalin 11 na dare shugaban masu garkuwar ya kira yana neman kudin fansa Naira miliyan 30 da kayan abinci da kwaya kafin su sako yaran.”

A cewarsa, iyalan sun roki a sassauta kudin zuwa abin da za su iya.

Kawo yanzu kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, SP Hassan Mansur, bai yi tsokaci kan lamarin ba.