Shugaban Kungiyar Malamai ta Najeriya (NUT) reshen Borno, Kwamred Garba Zali, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake biyan wasu malamai albashin N7,000 a jihar.
Ya ce, malaman da shafa sun tsinci kansu a wannan yanayi ne saboda hanyar batan fage suka bi wajen samun aikin karantawa a makarantun gwamnatin jihar.
Shugaban na NUT ya yi zargin cewa ba a bi tsarin da ya dace ba wajen daukar ma’aikatan da abin ya shafa.
Zali ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da horar da malamai 781 daga kananan hukumomi 19, a Kwalejin Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Umar Ibn Ibrahim Elkanemi da ke Bama.
- ’Yan bindiga sun shiga hannu wurin ba wa sojoji cin hanci a Taraba
- Masu garkuwa na neman N30m kan yara 3 a Kaduna
Ya ce masu daukar irin wannan albashin sun sami aikin ba ta hanyar da ta dace ba.
A cewarsa, wasu sun sami aikin ne ta hanyar cike gurbin malaman da suka yi ritaya da wasu da dama da aka dauka aiki ba tare da bin ka’ida ba.
Kwamared Zali, ya jaddada bukatar yi wa ɓanagaren ilimi gyara fuska a jihar Borno, musamman ma a matakin firamare.
Mataimakin gwamnan jihar Borno, Umar Usman Kadafur, ya jaddada aniyar gwamnatinsu wurin inganta malaman makarantu.
Ya ambaci yadda ake ware kudade domin shirya tarukan horarwa da kuma tsare-tsaren mayar da malaman da basu cancanci karantawa ba waɗansu ma’aikatun.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha, da kuma Ƙirƙira, Injiniya Lawan Wakilbe, ya bayyana cewa za a sake fasalin tsarin karantawa da kuma tantance ma’aikata, da kuma tsarin ƙarin ilimi da shirye-shiryen ci gaba ga malamai.