Kungiyar Manoma da Masu Kasuwancin Albasa ta Najeriya (OPMAN) ta yi barazanar daina kai albasa yankin Kudancin Najeriya daga ranar Litinin, matukar gwamnati ba ta amince da bukatunta ba.
Da yake ganawa da manema labarai a Jihar Sakkwato, Shugaban OPMAN, Aliyu Isa, ya ce mambobin kungiyar sun yi asarar albasa ta kimanin Naira biliyan 4.5 a sakamakon rikice-rikice a yankin Kudu.
“Bayan zama da tattaunawa da shugabannin kungiya suka yi, idan har gwamnati ba ta amsa kokenmu ba to za mu dauki wadannan matakai;
“Za mu daina jigilar albasa zuwa yankin Kudu baki daya daga ranar Litinin, 7 ga Yuni, 2021, sai gwamnati ta amince da bukatunmu,” a cewar Isah.
Daga cikin bukatunsu, kungiyar na so dole gwamnati ta biya mambobinta da suka yi asara a rikicin kabilanci da ya faru a yankin na kudu.
Sauran bukatun sun hadar da tabbatar da tsaro a yankunan da rikici ke yawan tashi, tare binciko musabbabin faruwar rikicin, da kuma wadanda suka farmaki mambobin kungiyar.
Kazalika, sun bukaci Al’ummar yankin na Kudu da su martaba kundin tsarin mulki da ya bawa ’yan Arewa damar yin kasuwancinsu a duk jihar da suke so.
A cewarta, a rikicin Abiya, kungiyar ta yi asarar mambobi uku, tirela 30, kananan motoci tara, rumbun ajiya 50 da buhu 10,000 na albasa.
A rikicin Shasa na Jihar Oyo, mutum 27 sun rasu, an kone tirela 5 da buhu 5,600 na albasa, sai motocin jigila 12 da aka kone.
Sannan an yi wa mambobin kungiyar fashin albasa ta kimanin ta Naira miliyan 13 a Jihar Imo.