✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masoyan Buhari sun mamaye Gidan Gwamnatin Najeriya a London

Magoya baya da masu adawa na gangamin yabo da kushe shugaban da ya je duba lafiyarsa a birnin London

A halin yanzu magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari sun mamaye Gidan Gwamnatin Najeriya da ke birnin London a kasar Birtaniya.

Magoya baya nasa sun mamaye Kofar Gidan na Abuja House ne, rike da alluna da kwalaye masu dauke da sakon fatan alheri ga Najeriya gami da yabo da jinjina ga Shugaban Kasar.

Hakan na zuwa ne a bayan da lokaci Reno Omokri, hadimin tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya jagoranci ’yan adawa masu gudanar da ta su zanga-zangar, inda suke faman kushe da yi wa salon jagorancin Shugaba Buhari Allah wadai.

Masu zanga-zangar ta adawa sun nemi Shugaban da ya koma gida Najeriya, wasunsu kuma suka yi cincirindo a bakin Asibitin Wellington inda Likitoci ke duba lafiyarsa.

Masu adawar sun bayyana hakan a matsayin barnatar da kudin talakawa masu biyan haraji, wasu kuma na sukar gwamnatin a kan rashin inganta bangaren kiwon lafiyar Najeriya da ya tabarbare.

Da dama da cikin al’ummar Najeriya sun bayyana bacin ransu kan tafiyar Buhari kasar Birtaniya ganin likita.

Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar Talatar da ta gabata ce Buhari ya tafi London ganin Likita kamar yadda aka saba.

Tafiyar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci a kasa suka tsunduma yajin aikin sai abin da hali ya yi saboda gazawar gwamnati na biyan bukatunsu.