Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta yin alkawarin raba gidaje da shaguna ga ’yan bindigar yan bindigar da suka addabe ta domin su ajiye makamansu.
Daraktan Watsa Labarai na Gwamna Aminu Bello Masari, Abdu Malumfashi karyata zargin a cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin.
Sanarwar ta yi karin haske ne kan wasu kalamai da aka danganta da Sakataren Gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa da suka jawo ce-ce-ku-ce.
A makon da ya gabata ne Mustaphan yayin amsa wata tambaya kan ko gwamnatin jihar za ta saka ’yan bindigar cikin wadanda za su ci gajiyar shirin tallafin da jihar za ta raba.
A nan ne sai ya kada baki ya ce, “Da farko dai mata muka so tallafa wa saboda yawancinsu an kashe mazajensu. Amma dole sai an samu zaman lafiya tukunna, yanzu gwamnati ba za ta iya yin komai ba”.
Sakataren Gwamnatin ya kuma ce har yanzu akwai dimbin Fulani da ke zaune cikin dazuka cikin mawuyacin hali amma suke fargabar shigowa cikin gari saboda fargabar tsangwama daga sauran jama’a.
Ya kuma ce gwamnatin na yunkurin sake tsugunar da irin wadannan Fulani da kuma ceto wadanda suke bukatar barin dazukan.
Jami’in ya ce yin hakan ne kadai zai dakile ayyukan ’yan bindigar daga yaduwa zuwa garuruwa kamar su Zakka, Dutsinma, Yantumaki, Matazu, Musawa, da sauransu.