Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya nemi gafarar al’ummar jihar bisa kura-kuran da ya yi a yayin mulkinsa.
Masari ya nemi afuwar ne ranar Litinin, lokacin da ake bikin kaddamar da Kwamatin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa da na Gwamna na jam’iyyar APC a jihar.
- Ba mu san inda A.A Zaura ya shiga ba – EFCC
- NAJERIYA A YAU: Barazanar Hari A Abuja: Abin da Gwamnati Ke Boyewa
Sai dai Gwamnan ya mayar da martani ga mutanen da ya ce sun yi wa gwamnatinsa da jam’iyyar APC butulci, saboda ba su samu dukkan abubuwan da suke nema ba 100 bisa 100.
A cewarsa, akwai wadanda suka sami kaso 80 wasu 70 kai har ma da masu kaso 50 amma duk ba su yi wa Allah godiya ba.
Kodayake Gwamnan bai kama suna ba, ana hasashen daga cikin wadanda yake yi ya shaguben har da tsohon Sakataren Gwamnatinsa, Mustapha Muhammad Inuwa, wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP bayan ya gaza samu tikitin takarar Gwamna a APC.