✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Oyo ta ba gwamnan Bauchi da matansa sarautun gargajiya

Daular Oyo, a karkashin Mai martaba, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi, ta ba Gwamna Isa Yuguda na Jihar Bauchi, sarautar Obasayero na Oyo.…

Alaafin Oba Lamidi Adeyemi ne nan tare da Obasayero Malam Isa Yuguda da daya daga cikin matansa, Hajiya A’ishatu Yuguda.Daular Oyo, a karkashin Mai martaba, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi, ta ba Gwamna Isa Yuguda na Jihar Bauchi, sarautar Obasayero na Oyo.
 Wannan shi ne karo na farko da aka nada bako a matsayin wannan sarauta ta “Obasayero”, wanda shi ne na 7 a cikin jerin wadanda aka ba wannan mukami, saboda irin gudunmawarsu ga hadin kan al’umma da ci gabansu.  
Matan Gwamna Yuguda su 4, su ma an ba su sarautun na gargajiya. Hajiya A’isha ta zama “Yeyeloyin”; Hajiya Mariya ta zama “Yeyeniwura”; Hajiya Abiodun, ta zama “Yeye”; a yayin da aka nada Hajiya Nafisa a matsayin “Yeyedunni.”
A al’ada, Alaafin din, bayan ya tabbatar da mukaman, sai ya sanya wa gwamnan babbar rigar saki da hula habar-kada, wacce ya lika mata wani ganye a gefen dama da hagu, tare da yin wasu abubuwa na al’adun gargajiya. Daga bisani, sai sabon Obasayeron ya yi gaisuwar ban girma, ta hanyar durkuso da mike kafafu tare da dafa hannaye kasa a gaban Alaafin. Su ma matan gwamnan duk sun bi sawun mijin nasu wajen daura sakakkun zannuwa da kalluba tare da yin irin wannan gaisuwa ta al’ada ga Alaafin din.
An shafe yinin ranar ana gudanar da bikin a gaban Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi da shugabar majalisar dokoki ta jihar, Hajiya Monsurat Sunmonu, wadanda suka jagoranci wasu manyan jami’an gwamnatin jihar, a harabar fadar Alaafin da ke Aganju Forecourt.
Wasu manyan sarakunan kasar Yarbawa da hamshakan attajirai da fitattun ’yan siyasa da manyan malaman addinai ne suka rufa wa Alaafin baya wajen karbar manyan baki, wadanda suka hada da sarakunan Bauchi da Katagum da Dass da Ningi da Misau da Jama’are da shugaban majalisar dokoki ta Jihar Bauchi da ’yan majalisar da wasu kusoshin gwamnatin Jihar Bauchi da wasu fitattun ’yan siyasa da shugabannin hukumomi.
Cikin jawabinsa Alaafin na Oyo, Oba Lamidi ya ce masarautar Oyo ta yanke shawarar nada Gwamna Isa Yuguda bisa wannan sarauta ne saboda lura da irin kyawawan halayen dattaku da kaunar jama’a ba tare da nuna kyama da bambancin kabila ko addini ba da yake da su.  Haka nan an lura da fafutukar da yake yi ta ganin an samu ci gaban al’umma da dunkulliyar kasa, kamar yadda marigayi Firayiminista, Sa Abubakar Tafawa balewa ya gudanar da salon mulkinsa a lokacin yana raye.
“Dangantakar farko da ta hada ni da Malam (Dokta) Isa Yuguda ta faro ne a cikin shekarar 1979 a lokacin yana aikin bautar kasa a nan cikin garin Oyo, wanda a duk lokacin da suka shigo fada tare da abokan aikinsa ina yi masa addu’o’in samun nasarar rayuwa da daukaka. A dalilin kauna da soyayyar al’ummar Jihar Oyo, Gwamna Yuguda ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 10 domin tallafa wa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a shekara ta 2011.” inji Oba Adeyemi.
Da yake karanta gajeren jawabin amincewa da karbar sarautar, Matawallen Bauchi kuma Ardon Chikin Gidan Dukku, Gwamna Isa Yuguda, ya yi murna da girmamawar da Alaafin ya yi masa da matansa hudu (4), wanda ya ce, girma ne ga daukacin al’ummar Jihar Bauchi. “Gwamnatinmu tana da yakinin wanzuwar ci gaban Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa mai cikakken ’yanci da kwanciyar hankali da ingantaccen tattalin arziki. Domin mu nuna hakan a aikace, gwamnatinmu ta soke salon daukar wadanda suka fito daga wasu jihohi aiki a matsayin kwantaragi. Duk ’yan Najeriya, ba tare da lura da jihohinsu na asali ba, yanzu ana daukarsu aikin gwamnati a matsayin cikakkun ma’aikata da ake biyansu fansho a Jihar Bauchi. Yanzu haka mun bayar da guraben aiki na mataimaka na musamman da masu bayar da shawarwari guda 50 da suka fito daga wasu jihohin kasar nan. Shi kansa mai magana da yawun gwamnati (Chief Press Secretary) dan asalin Ogbomoso a Jihar Oyo ne.” inji shi.
Daga nan sai ya bayar da tabbacin ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya da ingantattun shawarwari ga Alaafin domin ci gaban masarautar da kasa baki daya.
Cikin mashahuran mawakan da suka halarci bikin akwai King Sunny Ade, wanda ake wa kirarin Sarkin Sarakunan mawakan Yarbawaya.  Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Dokta Omololu Olunloyo da Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Mai Yasin, suna cikin manyan mutanen da suka halarci bikin.