✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Masarautar Kano: Yadda Coronavirus ta sauya hawan Sallah

Tun daga lokacin da aka nada sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Masarautar ta shiga shirye-shiryen gudanar da hawan Sallah. Sanarwar da Gwamnatin Kano…

Tun daga lokacin da aka nada sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Masarautar ta shiga shirye-shiryen gudanar da hawan Sallah.

Sanarwar da Gwamnatin Kano ta yi cewa ba za a gudanar da bukukuwan sallah a jihar ba sakamakon annobar coronavirus, ta jefa Jama’a cikin damuwa cewa lamarin zai shafi hawan Sallah a dukkanin masarautu biyar da ke fadin jihar.

Shirya Hawan Sallar Sarki Aminu na farko

Malam Yahaya Bello Gwangwazo hadimi ne ga Sarkin Dawakin Tsakar Gida kuma Hakimin Kunbotso Alhaji Ahmad Ado Bayero ya bayyana cewa masarautar ta so ta gudanar da bukukuwan sallah don mutane su fito su ga Sarkin da suke so.

Aminiya ta samu rahoto cewa tun daga lokacin da gwamnatin jihar ta nada sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, masarautar ta shiga shirye-shiryen gudanar da hawan sallah.

Sai dai haka ba ta cimma ruwa ba sakamako bullar cutar coronavirus a jihar.

Coronavirus ta bata shiri

“Gaskiya mun so gudanar da bukukuwan salla musamman ma yadda mutane suke ta burin za su fito su ga sarkin da suke so.

“Kun san mutane suna masa kallon mahaifinsa. Sai dai Allah bai nufi hakan ba sakamakon wannan annoba ta kurona.

“Dama haka Allah Yake lamarinsa – kana taka Allah Yana tasa,” ya shaida wa Aminiya.

‘Hawan Sallar Sarki a mota?’

A cewarsa “Abin da kawai za mu iya gudanarwa shi ne za a fita masallaci da kafa za kuma a dawo a mota a maimakon yin amfani da dunkuna da aka saba a baya.

“Ta wannan hanya ce kadai masoyan Sarkin za su iya ganinsa a,” a cewarsa.

Ba haka aka so ba

Ashari Kamfa makusancin Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ne. Ya bayyana cewa lallai ba su ji dadi yadda aka yi sallar wannan yanayin ba.

A cewarsa, sun riga sun shirya gudanar da bikin sallah musamman duba da cewa wannan ne karon farko da sabon sarki zai gudanar da bikin sallah a fadarsa.

“Gaskiya an ci buri na shirye-shiryen gudanar da bikin sallah. Amma sai ga lamarin annobar cutar korona ta hana.”

Sai wane lokaci?

Malam Yahaya ya ce suna sa ran gudanar da bukukuwan sallah a lokacin Babbar Sallah.

“Muna sa rai mu gudanar da hawan sallah a lokacin babbar sallah idan Allah Ya kai mu.

“Muna fata kafin zuwan wannan lokacin wannan annobar ta tafi gaba daya,” inji shi

Ai hawan salla shi ne babban shagali

Wasu jama’ar jihar sun nuna rashin jin dadinsu game da yadda aka hana gudanar da bikin salla a jihar.

Malam Ibrahim Bashir ya ce sallar bana ta zo a wani yanayin da ba a so.

“Batu na gaskiya sallah a wannan yanayi babu dadi domin shi hawan sallah shi ne abin da yake kara nuni da shagulgulan bukukuwan sallah a jihar,” inji shi.

Sai da lafiya ake shagali

“Komai sai da lafiya ake yin sa.  Babu abin da za mu ce sai godiya ga Allah. Muna jiran babbar sallah,”  a cewar Amina Aminu.

Aminiya rawaito cewa a ranar Asabar jim kadan bayan Sarkin Kano ya bayar da sanarwar yin sallar Idi a jihar, sai aka buga bindiga wanda ke cikin alamomin da ke nuni da fara gudanar da bukukuwan sallah a jihar”.

Ba kan Sarki Aminu farau ba

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Sarki bai gudanar da hawan sallah ba.

Gabanin Sarkin Kano Aminu mai ci, Sarki Muhammadu Sunusi II a shekarar da aka nada shi bai gudanar da hawan  sallah ba sakamakon hare-haren ‘yan tayar da kayar baya na Boko Haram.

Sai da lokacin Babbar Salla ya zo sannan aka yi, kamar yadda wani dogari a masarautar ta Kano wanda ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya.

%d bloggers like this: