Masarautar Bauchi ta tube rawanin wasu sarakai shida a yankin Hakimin Galambi.
Jami’in yada labaran masarautar, Babangifa Hassan Jahun ya ce majalisar masarautar ta soke nadin sarakan da abin ya shafa ne saboda Hakimin Galambi bai bi ka’ida ba wajen nada su.
- ’Yan banga sun kashe ’yan bindiga a Kebbi
- Bayan ganawa da ’yan TikTok, Hisbah ta gayyaci ’yan Kannywood
Ya kara da cewa masarautar ta dakatar da Haikimin ne Hakimin Galambi, Alhaji Shehu Adamu Jumba daga yin nadin sarauta na tsawon shekara guda, daga ranar 7 ga watan Nuwamba, sannan wajibi ne ya bi ka’ida nan gaba wajen yin nadin sarauta.
A kwanakin baya ne Hakimin Galambi wanda shi ne Danlawal na Bauchi, ya yi wa wasu mutanen shida nadin sarautar Galadaman Danlawal, Wakilin Dokan Danlawal d kuma Majidadin Danlawal.
Sauran su ne Wakilin Gonan Danlawal, Sarkin Dajin Danlawal da kuma Hardon Danlawal.