✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan ganawa da ’yan TikTok, Hisbah ta gayyaci ’yan Kannywood

’Yan  Kannywood sun bayyana rashin jin dadi kan hanyar da Hisbah ta bi wajen gayyatar su

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta gayyacu jaruma da furodusoshi da darakatocin fina-finan Hausa na Kannywood, mako guda bayan ta gana da ’yan TikTok.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah (bangaren ayyuka) Dokta Mujahideen Aminudden ya bayyana cewa Hukumar na son ganawa da ’yan Kannywood ne don tattaunawa a kan abin da ya shafi gyaran sana’arsu.

Dokta Mujahideen ya ce kamar yadda aka samu fahimtar juna hukumar da ’yan TikTok a makon da ya gabata, suna sa rai tattaunawar da ’yan fim zai haifar da kyakkyawan sakamako.

“Muna neman jarumai da masu shirya fiina-finai da masu bayar da umarni..da duk wasu da ke yi wa fim hidima ban da mawaka.

“Muna sa rai tattaunawar tamu za ta haifar da alheri kamar yadda waccan tattaunawarmu da ’yan TikTok”

’Yan Kannywood ba su jadi ba

Sai dai kungiyar Jarumai ta Kannywood ta nuna rashin jin dadinta game da hanyar da Hisbar ta bi wajen gayyatar su inda ta nemi Hisbar da ta gyara kuskuranta.

Shugaban kungiyar, Alasan Kwalle, ya bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da za su yi zama da Hisbah ba, don haka suna maraba da gayyatar.

“A lokuran baya mun zauna da Hukumar Hisbah inda suka ba mu shawarwarin a kan sanaarmu.

“Sai dai a wannan karon maimakon Hisbar ta bi hanyar da ta dace wajen gayyatar tamu, amma sai muka tsinci sanarwar a rediyo, wanda a ganinmu hakan ya yi kama da neman masu laifi.

“Kamata ya yi Hukumar Hisbah ta aiko mana da takarda ko kuma ta neme mu ta hanyar Hukumar Tace Finafinai. Muna da Kumgiyoyi daban-daban wanda kuma akwai babbar kungiyarmu,” in ji shi.

Ya ce duk da hakan masu ’yan  fim din za su amsa kiran kamar yadda ta nema inda ya ce a “yanzu ma a shirye muke mu amsa gayyatar Hukumar muddin dai Hukumar za ta gyara kuskurenta.