A karshen mako jiya ne aka yi bikin nada Mai bai wa Gwamnan Jihar Nasarawa Shawara kan Harkokin Nakasassu Hajiya Hajara danyaro a sarautar Ta-Fisun Ara da ke karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Nasarawa. Mai martaba Sarkin Ara Alhaji Ibrahim Galadima ne ya nada ta sarautar Ta-Fisun Ara.
A jawabinsa, Mai martaban bayan nadin sarautar ya ce masarautarsa da al’ummar yankin baki daya sun yi la’akari ne da gagarumar gudunmawa da taimakon da Hajiya Hajara danyaro ke bai wa al’ummar yankin baki daya musamman marasa galihu da nakasassu ya sa masarautar ta yanke shawarar nada ta wannan sarauta.
Ya bukaci mutanen yankin musamman mata su yi koyi da kyawawan ayyukan tallafi da Hajiya Hajara danyaro ke yi musamman wajen taimaka wa al’umma a duk matakai musamman nakasassu don inganta rayuwarsu., Ya ce ba shakka ta cancanci sarautar kamar yadda a cewarsa sunan sarautar ta nuna din ita tafi kowace mace a yankin idan ana batun taimako da bauta wa al’umma ne.
Wadansu daga cikin abokan arziki da manyan ’yan siyasa da sauransu da suka halarci bikin, sun yaba da sarautar da masarautar ta bai wa Hajiya danyaro inda suka yi mata fatan alheri.