✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Agege ta karrama Kwankwaso a Legas

Masarautar Agege ta karrama tsohon Gwamnan Jihar Kano,  Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sarautar Garkuwan Kurmi, a wata sanarwa…

Masarautar Agege ta karrama tsohon Gwamnan Jihar Kano,  Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya sanata Rabiu Musa Kwankwaso da sarautar Garkuwan Kurmi, a wata sanarwa da kakakin majalisar masarautar ya fitar a karshen makon jiya, Alhaji Ali Dinar. Masarautar ta karrama Kwankwaso ne sakamakon irin uwa da makarbiyar da yakan yi a kan matsalolin da kan taso wa ‘yan Arewa mazauna Kurmi.
 “Mun samu matsaloli a garin Fatakwal mai girma Kwankwaso ne ya warware mana, a kwai wani lokaci da aka kame mana mutane  a Legas, haɗuwa kawai mai martaba ya yi da Kwankwaso a tashar jirgin sama da ya shaida masa halin da ake ciki,  sai ya kira Gwamanan Legas na wanccan lokacin Fashola ya shiga aka wareware matsalar, sannan yanzu da wannan rikici na mil 12 ya taso mana babu wanda ya kawo mana ɗauki kamar Sanata Kwankwaso, duba da waɗannan hidindimu da yake yi wa talakan Kurmi ne muka ba shi wannan sarauta, ta Garkuwan Kurmi, domin yaba kyauta tukwici ne, “ inji shi.
Alhaji Ali Dinar ya shaida haka ne a lokacin da Kwankwaso ya yi taron miƙa ragowar ɗaurarrun mil 12  talatin da ɗaya da ya karɓi belin su ya  miƙa su ga masarautar ta Agege da shugabannin kasuwar mil 12 a ƙarshen makon jiya.
Alhajidanjuma Yakubu, Hakimin Gabas, dan iyan Agege ya shaida wa Aminiya cewa, masarautar Agege ita ce mafi dadewa da tsohon tarihi a daukacin jihohin Kurmi, domin ta kafu tun a shekarar 1863,  kuma Turawa sun tarar da ita ne sannan suka yi mata takardar shaida tun a wanccan lokacin. Don haka ita ce masarautar da tafi cancanta ta bai wa Sanata kwankwaso wannan sarauta a daukacin masarautun  jihohin Kurmi.
Shugaban ƙungiyar ‘yan Arewa ta Arewa consultatibe forum, Alhaji Ado dansudu  ya shaida cewa a yanzu  ‘yan Arewa mazauna Kurmi ba su da wani wanda suke bugun ƙirji da shi, wanda suke kai wa kukansu ya share musu hawaye tamkar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, don haka ya cancanci a yaba masa.
A jawabin da ya gabatar Sanata Kwankwaso ya gode wa Allah da ya ba shi ikon yin belin mutane 71 da suka rage a daure, wadanda suka shafe sama da watani 4 a tsare, waɗanda suka hada  da yara ƙanana daga jihohi daban-daban na Arewa da wani dattijo dan garin Ijebu Ode a Jihar Ogun da yake yin dako a kasuwar mile 12, da Bayaraben Jihar Kwara da wani matashi dan yankin Neja-Dalta,  ya ce zuwansa Legas na 10 ke nan a kan wannan lamarin .
 “Wadannan mutanen marasa galihu ne da ya zama wajibi a taimaka musu a karbi belinsu, domin ba su da gatan wanda zai tsaya musu. A hakan ne mutum uku daga cikin su suka rasa ransu a kurkuku, kuma za mu yi ƙoƙari   don ganin an bi musu haƙƙinsu,” inji shi.
Ya kuma shawarci mutanen da ya karbi belin nasu da su kasance ‘yan kasa nagari a duk inda suke, ya kuma bai wa kowannen su Naira dubu 20, domin su koma gida su huta. Mutane 31 da aka karbi belin nasu sun yi jawabin godiya ga Sanata Kwankwaso a lokacin da wasunsu suka yi ta shararara kukan murna, suna cewa ba su zaci za su fita daga kurkukun ba har sai da Allah ya kai musu dauki ya turo musu Sanata Kwankwaso.
Bayan da Sanata Kwankwaso ya kammala taron ne ya ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira da ke Karar shanu ta Isheri a Jihar Ogun, tare da Sarkin Agege Alhaji Musa Dogonkadai  da tawagarsa, inda suka gane wa idanunsu halin da ‘yan gudun hijirar da suka yiwo kaura daga garuruwan Arewa maso Gabas suke ciki, Kwankwason ya tallafa musu ganin irin halin da suke ciki, kana ya yi kira ga ‘yan Arewa  masu hannu da shuni da ke Kurmi da na Arewa da su waiwayi ‘yan gudun hijirar, domin su taimaka musu da abin da Allah ya hore musu.