A ranar Alhamis ce Majalisar Dattawa ta amince da kudurin kafa Hukumar Raya yankin Arewa maso Yamma domin magance matsalolin da yankin ke fuskanta.
Kudurin ya zama dokar ce bayan majalisar ta amince da rahoton Kwamitin Ayyukan na Musamman a kan kafa hukumar ta NWDC.
- Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Senegal Bassirou Faye
- Auren Marayu: Limamai sun yi wa Ministar Tinubu wankin babban bargo
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne tare da wasu sanatoci guda 20 daga jihohin yankin guda bakwai suka gabatar da kudurin na kafa hukumar.
Shugaban Kwamitin, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan Jam’iyyar APC, mai wakiltar mazabar Borno ta Tsakiya ne ya bukaci majalisar ta saurara rahoton domin amincewa, sannan Sanata Ireti Kingibe ‘yar Jam’iyyar LP mai wakiltar Abuja ta goya masa baya.
Da yake gabatar da rahoton, Sanata Kaka ya ce an tsara tare da gabatar da dokar kafa hukumar ce domin bunkasa tattalin arzikin na Arewa maso Yamma.
Ya kara da cewa samar da sabuwar hukumar za ta taimaka wajen kara kusanto da Gwamnatin Tarayya zuwa ga yankin domin biya wa mutane bukatunsu.
Sai ya bukaci sanatoci su amince da kudurin domin ta zama doka.
Da aka kada kuri’ar amincewa da kafa hukumar a karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, dukkan sanatocin da suke zauren majalisar ne suka amince.
A jawabinsa jim kadan bayan kuri’ar, Sanata Barau ya yaba wa sanatocin bisa goyon baya da suka ba kudurin har aka amince da shi.
Idan aka kafa hukumar, za ta taimaka wajen magance matsalolin da yankin ke fuskanta da ma kasar baki daya.
Da yake bayyana yankin a matsayin mai yalwar kasar noma, ya ce hukumar za ta yi aiki ka’in da na’in wajen gyarawa tare da dawo da martabar wasu ababen more rayuwa da ‘yan ta’adda suka lalata.
“Don haka idan lallai muna so a yi noma kasarmu ta wadata da abinci, dole mu samar da abubuwan da ake bukata domin bunkasa bangaren da ma sauran bangarori masu muhimmanci.
“Lallai akwai buƙatar kafa hukumar nan. Na yaba da goyon bayan da kuka bayar; babu wanda ya ki aminta. Kowa ya amince da kafa ta.
“Yanzu za mu aika ta zuwa ga Shugaban Kasa domin ya amince, ya rattaba hannu,” inji shi.