✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masar ta gayyato zaratan ’yan kwallo don karawa da Eagles

A shirye-shiryen tunkakar wasan da Masar za ta yi da Super Eagles a kokarin hayewa gasar cin kofin Afirka wanda za a yi a ranar…

A shirye-shiryen tunkakar wasan da Masar za ta yi da Super Eagles a kokarin hayewa gasar cin kofin Afirka wanda za a yi a ranar 25 ga wannan wata a Kaduna, kocin kungiyar kwallon kafa ta Masar Hector Cuper ya gayyato zaratan ’yan kwallon da suke wasa a sassan duniya don karawa da Najeriya.
Daga cikin zaratan ’yan kwallon da kocin ya gayyato akwai Mohammed Elneny na Arsenal da ke Ingila da Mohammed Salah na AS Roma da ke Italiya.
Sauran fitattun ’yan kwallon da kocin ya gayyato sun hada da Ahmed Hassan na Sporting Braga, da Mahmoud Trezekuet na Anderletch da ke Beljiyam da kuma Amr Warda na Panetolikos na Girka.
Ana sa ran ’yan kwallon da kocin ya gayyato za su hadu ne da takwarorinsu da ke wasa a gida a sansanin horar da su a ranar 20 ga wannan wata da muke ciki.
Kocin ya ce ya yanke shawarar gayyato biyar ne daga cikin ’yan kwallonsa da ke yin wasa a waje yayin da kocin Super Eagles Samson Siasia aka ruwaito ya gayyato akalla ’yan kwallo 20 daga waje.
Za a yi wasan farko ne a ranar 25 ga wannan wata a Kaduna yayin da wasa na biyu kuma zai gudana ne a ranar 29 ga wannan wata a filin wasa na Borg El-Arab da ke Aledandria na Masar.
Tuni Hukumar NFF ta sanar da kudin tikitin shiga filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna.  An sanya Naira dubu 1 a wurin manyan baki yayin da za a biya Naira 300 a bangaren ya-ku-bayi.