Barkanmu da sake saduwa da ku iyayen gida a cikin wannan filin namu na girke-girke. Tare da fatar ana lafiya kuma ana gwada duk irin nau’o’in girke-girken da muke kawo muku. A yau na kawo muku yadda ake hada masar dankali ce a sha karatu lafiya.
Abubuwan da za a bukata
- Dankali
- Attarugu
- Albasa
- Kwai
- Gishiri da magi
- Kori
Hadi
Bayan uwargida ta fere dankalinta, sai ta dora shi a wuta ya nuna ya yi luguf sosai. Sannan ta dauko roba ko kwano mai zurfi ta zuba a ciki. Sai uwargida ta debo kwai mai dan dama ta fasa a kan dankalin. Sai ta samu ludayi ta dama dankalin da kwan har sai sun hadu sosai. Sai a debo albasa da attarugu a jajjaga su sannan a zuba a kan hadin dankalin da magi da gishiri da kori daidai dandano sannan sai a sake dama hadin domin kayan hadin su shiga dankalin sosai.
Idan uwargida ta gama, sai ta dauko tanda ta dora a kan wuta. A zuba man gyada a kowace gurbi sannan a debo kullun dankalin a zuba a kowace gurbin tandar. Sai a dan ba kullun mintuna domin cikin masar ya nuna. Idan gefe daya ya yi, sai a sake juya wainar zuwa daya gefen har sai ta nuna kafn a sauke.