✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masana’antar Kannywood za ta dauki shekaru kafin ta koma hanyacinta – Hassana Dalhat

Wata mai dillanci da tallata fina-finan Kannywood, Hassana Dalhat, ta ce masana’antar za ta shafe tsawon lokaci tana fama da kalubale kafin ta samu damar…

Wata mai dillanci da tallata fina-finan Kannywood, Hassana Dalhat, ta ce masana’antar za ta shafe tsawon lokaci tana fama da kalubale kafin ta samu damar farfadowa.

Hassana Dalhat ta ce hakan zai fi shafar hanyar samun kudin shiga wa ita kanta masana’antar.

Cikin wata ganawa da jaridar PREMIUM TIMES a Kaduna , ta ce lamarin ya kara muni ga masu harkar dillancin fina-finai da tallata su musamman bayan da aka bullo da nuna fina-finai a gidajen sinima.

“Da dama cikin masu ci a harkar yanzu suna rayuwa ta babu. Babu kasuwa sam-sam, ka je shagunan fim a Kano da Kaduna. Wasu daga sun riga sun bar harkar saboda babu fina-finan da za a sayar. Su ma masu hada fina-finan suna tafka hasara; don haka sun daina ci da sana’ar.

“Bari in fada muku cewa, a duk tsawon rayuwata na kasance mai dillanci da tallata fina-finan Hausa. Ina sane da yanayin masana’antar fim din, yanayi ne na ha’ula’i ga mafi yawan masu dillancin fina-finan tunda aka fara amfani da gidajen sinima.

“Kai hatta masu shiryawa da masu hada fina-finan ba sa farin ciki da haka. Sai dai maganar gaskiya ba za su iya yin wani katabus game da batun ba. Satar fasaha ta cinye dunduniyar masana’antar gaba daya, don haka kusan kowa likkafarsa ta ja baya.

Tunda su masu kula da harkar da mu jaruman ba ma iya gano bakin zaren, sai kawai muka fawwala lamarin ga Mai duka. Fina-finan ana nuna su ne a gidajen sinima kawai. Na yi m agana da furdusoshi da dama wadanda suka kai fina-finansu sinima. Hasara kawai suke tafkawa. Mutanenmu ba su saba da sinima ba. Ina nufin ainihin masu kallon fim ba mutane ne masu zuwa sinima ba. Sun fi son su sayi fim sa’annan su koma gida su kalla,” inji ta.

Ta kara da cewa, “Kai koda matan gida ma kan nuna fim bayan sun karbi hayar fim din a farashi mai rangwame. Amma yanzu duk wannan ya kau.”

Batun hada fina-finai

H assana ta ce yayin da masu hada fina-finan ke fadi-tashin hada fina-finan domin nuna su a gidajen sinima, sai dai a batun hada fim na kara zama da wahala a Kano.

“Masu kudi ne kawai cikinsu a yanzu suke iya hada fim. Hakan shi ne gaskiyar lamari, kuma a hakan ma sai ka yi ta rokon mutane kan su je kalli fim din naka. Ba abu ne mai kyau ga masana’antar ba. Yanzu kuma ga cutar Kurona ta shigo ta kusan durkusar da komai; kuma ba ni da tabbas cewa koda bayan al’amura sun lafa ko za su koma hada fina-finan,” inji ta.

Ta ce, “Kwanakin nan Rahama Sadau ta fitar da fim dinta mai suna, ‘Mati a Zazzau’, kana iya ganin yadda take kai-komo wajen rokon mutane su taimaka su je su kalli fim din. A yanzu galibin furodusoshi sun koma hada fina- finai ga tashoshin talabijin. Za su hada fim din sannan su sayar da shi ga tashoshin domin su haska shi. Kai muna kan ganiyar rasa na yi fa,” injita

Mafita

Hassana ta nuna akwai mafita guda daya tak, inda ta ce sai dai in har masu zuba jari ko kamfanoni da kuma gwamnati za su saka jari a harkar. “Ya kamata gwamnati ta shiga ciki, koda kuwa matakin gwamnatin jiha ce. Zai iya zama hanyar samun kudin shiga ga gwamnatocin jihohi kuma matasa su samu aikin yi.

“Musamman yankin Arewacin kasar nan, lura da dimbin jama’ar da yankin ke da shi, shakka babu yana bukatar haka. Kuma lokaci na neman kurewa,” inji ta.