✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masallacin Harami ya karyata bidiyon kiran Sallah daga cikin Ka’aba

Hukumar gudanarwar Masallacin Harami ta karyata bidiyon da ke riya cewa an ji kiran Sallah da Sallar Jam'i daga cikin Dakin Ka'aba.

Hukumar gudanarwar Masallacin Harami a kasar Saudiyya ta karyata bidiyon da ake yadawa cewa an ji kiran Sallah daga cikin Dakin Ka’aba.

Hukumar Masallacin Harami ta karyata bidiyon ganin yadda aka yi ta yada shi a kwanakin baya, cewa masu Dawafi a masallacin sun ji sautin kiran Sallah da kuma Sallar jam’i na fitowa daga cikin dakin Ka’aba, amma ko da aka shiga ciki ba a ga kowa ba.

Masallacin Harami ya sanar a ranar Juma’a ta ce, “Bidiyon da ke yawo a kafofin sada zumunta game da “abin da hankali ba zai dauka ba” daga cikin Ka’aba karya ne.”

Sanarwar, ta shafin Facebook na masallacin ya ci gaba da cewa, “Bidiyon na watan Ramadan ne a lokacin da aka bude dakin Ka’aba ga daya daga cikin Shugabannin Musulmi da suka ziyarci Harami [domin Umrah]”.

Bidiyon karyar da aka yi ta yadawa da harsuna daban-daban ya karade gari, ya kuma yi tashe a kafafen sada zumunta.

Lamarin bidiyon karyan dai ya tayar da kura, inda wasu ke ganin abin a matsayin babban abin al’ajabi, wasu kuma ke ta bayyana shakkunsu game da shahihancinsa.

 A lokuta da dama a kan samu mutane sun kirkiri bidiyo ko sauti ko kuma hoto, galibi domin ci-ma wasu manufofinsu.

Masu irin wannan dabi’ar suka yi ne domin abin da suka yi ya yi tashe ko su samu mabiya ko martani ko ba ta suna da sauransu a kafofin sada zumunta.