Labarin masallacin da ake sallar juma’a sau biyu a unguwar Markas a Agege da ke garin Legas ba sabon abu ba ne ga hausawan Agege domin an yi kusan shekaru goma ana wannan dambarwa tun bayan bijirowar wata taƙaddama da ta sanya aka rufe masallacin na tsawon kimanin shekaru tara.
Malam Adamu Abdulƙadir wanda ya ce an haife shi ne a wani gida da ke daura da masallacin, ya shaida wa Aminiya cewa ko da ya taso ya riski masallacin a gine, kana sun samu labarin cewa wadansu ɗaiɗakun masu hannu da shuni ne na Hausawa suka gina masallacin kuma Sheikh Abubakar Gumi ne ya aza harsashin gininsa, kodayake a wanccan lokacin bayanai sun nuna ba a kafa ƙungiyar Izala ba, amma ba a yin wazifa ko wani abu dake nuna alamun masallacin na ’yan ɗariƙa ne. “A wancan lokacin Malam Harisu ne ke limanci a masallacin sai daga bisani wadansu mutane suka bijire masa a dalilinsu na rashin yarda da shi, domin a cewarsu, yana yin wadansu abubuwa da suka saɓa wa aƙidunsu, kamar zuwa maulidi da makamantan haka. Sai suka yi yunƙuri tsige shi daga limancin, abinda ya sanya zuwa kotu, daga nan kotun ta ba da umarnin rufe masallacin har sai da ya yi shekaru 9 a rufe. Sai liman Harisu ya cigaba da bada sallar a ƙofar gidan Baƙon Nana a kan titin Alfanla wadda ba shi da nisa daga masallacin.’’
“A wanccan lokacin akwai wadansu ’yan uwan juna yaya da ƙani, waɗanda fitattune a Legas da suka jiɓanci al’amarin masallacin kuma kowane ɗayansu na mara wa ɗaya ɓangaren da ke rikici a kan masallacin, inda marigayi Sarki Jubrila Abdallah ke goyon bayan ’yan ɗarika, a ɗaya ɓangaren kuma ƙaninsa marigayi Alhaji Abu Abdallah yake mara wa ’yan izala baya. Ƙoƙarin shugabanni ne ya sanya kotun ta bada umarnin sake buɗe masallacin, inda aka yi aikin gayya aka nome ciyayin da suka fito, domin a wannan lokacin mun yi ta cin karo da macizai da sauran ƙwari, a haka muka yi ta aikin gyaran masallacin, ganin yadda ya ɗauki tsawon shekaru a rufe,” inji shi.
Ya ce a lokacin da kotun ta ba da umarnin buɗe masallacin ‘yan kungiyar Izala ne suka fara ba da sallar juma’a a masallacin, inda limamin nasu ya yi fatawar cewa duk wanda ya yi sallar juma’a ta biyu ba shi da sallah. “A wancan lokacin ’yan ɗarika ba su yi sallah ta biyu ba a masallacin sai suka sake garzayawa kotu inda kotun ta ba da umarnin cewa limamin da yake jan sallah tun da fari kafin a rufe masallacin shi ke da hurumin yin sallar juma’a ta farko a masallacin, sai idan bayan su idar ne masu adawa da shi za su yi tasu, to a haka ne liman Harisu limamin ɓangaren ’yan ɗariƙa yake jagorantar sallar juma’a ta farko a masallacin, wanda ake fara huɗuba daga ƙarfe 1:30 a idar da sallar zuwa ƙarfe 2:10, yayin da su kuma ’yan izala ke yin tasu daga ƙarfe 2:15 zuwa ƙarfe 3. Masallacin kan cika maƙil har haraba da waje a sallar farko, yayin da a sallar juma’a ta biyu ba a wuce sahu ɗaya da rabi zuwa biyu, sai idan ana hutu ne kowa na gida suke cika sahu uku, domin da yawa daga cikin ’yan izalar ma ba sa yin sallar juma’a ta biyun, sakamakon fatawar da suka rigaya suka ji na cewa babu juma’a ga wanda ya bi sallah ta biyu. Sauran salloli biyar kuwa ’yan ɗariƙa ne kawai ke yi a masallacin.’’
“Abin sha’awa shi ne, kiraye-kirayen da shugabanni ke yi na a kai zuciya nesa ne ya sanya ba a taɓa samun wani tangarɗa ba, domin a lokcin da limamin ’yan ɗarika Malam Ayuba ke ba da sallar juma’a, idan zai fita yakan haɗu da limamim ’yan izala shi kuma ya shigo zai ba da sallah sai yaj e su gaisa cikin girmamawa da walwala, abin da wadansu ke cewa shi ne ya sanya ƙungiyar Izalar ta sauya limamin nata, ta sanya wanda ba ya yarda ma a haɗu da shi balle a gaisa,” inji shi.
Wannan masallaci mai hawa biyu wanda shi ne mafi girman farfajiya da haraba a jihar Legas, ya faɗa cikin yanayi na rashin kulawa ta yadda a baya ruwan sama kan hana yin sallah, domin ruwa kan cika shi sakamakon daɗewa da ya yi a rufe, kuma babu wata ƙungiya ta take jan ragamar gyaransa bisa dalillan taƙadammar da ake yi a kansa. A cewar Malam Adamu Abdulƙadir, a baya-bayan nan ne wani attajiri mai suna Alhaji Abu Ilori ya kai wa masallacin ɗauki, inda ya ware miliyoyin nairori da a ka yi ta gyaran masallacin da su kuma a yanzu an kusa kammala aikin, kaɗan ya rage a ƙarasa, sannan akwai maganar cewa idan an kammala za a gayyato Mai martaba Sarkin Kano Malam Sunusi Lamiɗo Sunusi ya buɗe masallacin, “a lokacin da wannan attajirin ya yunƙuro zai gyara masallacin su ’yan ƙugiyar Izalan sun so su hana shi bisa dalilansu na cewa har zuwa yanzu maganar masallacin na kotu, kuma sun ɗauka wata ƙungiya yake yi wa gyaran, sai ya tabbatar masu da cewa ai shi don Allah yake yi, duk sanda aka gama shari’ar masallacin duk ƙungiyar da aka bai wa masallacin sai ta rike, shi dai ya yi ne saboda Allah,” inji Malam Adamu.
Bayanan da Aminiya ta tattara sun nuna cewa har yanzu maganar masallacin na gaban kotu kuma a duk wata a kan bai wa lauyoyi na goro a kan shari’ar daga cikin kuɗin da ake neman taimako a wurin jama’a, kuma da yawa daga cikin masallatan da muka tattauna da su na dukkan ɓangaren sun nuna rashin jin daɗinsu da wannan turka-turkar.
Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin masarautar Agege da masu kula da masallacin, amma sai suka ce ba za su ce komai ba, domin a halin yanzu maganar na gaban kotu, sai dai fatan masarautar ta Agege shi ne a samu daidaito a wannan dambarwar ta yadda za a dinga yin sallar juma’a ɗaya kamar yadda ake yi a sauran masallatai.
Gaba dayansu ba su da sallah – Sheikh Zakariya Yawale
A fatawar da ya bai wa Aminiya a kan wannan al’amari, Sheikh Hussaini Zakariya Yawale, wani malami a Abuja, ya ce musulunci bai ba da damar a rika yin sallar jam’i biyu a masallaci guda ba, na juma’a ne ko kuwa na yau da kullum. Ya ce, “Aikata hakan raba kan al’ummar musulmi ne, shi ko raba kan musulmi kafirci ne. Abin da ya kamata kotu ta yi shi ne ta binciki su wane bangare ne su ke da ikon mallakar masallacin ta hanyar gano wadanda su ke da ikon mallakar filin da kuma gina shi a farko, sannan kuma su wane ne mazauna unguwar ko wadanda ke da rinjaye a wajen a tsakanin bangarorin biyu, duk wadannan abubuwa ne da ya kamata kotu ta yi la’akari da su.’’
“Idan kotun ta gano masu masallacin sai ta ba su kariya da jami’an tsaro, sannan ta hana wani bangare da ba su da damar yin wani jam’i a wajen, idan ko kotun ta gaza gano masu masallacin, sai ta hana bangarori biyun jam’i a masallacin, ta kuma ba da umarnin a rusa shi, don magance matsalar rarrabuwar kan al’umma da kuma kawo tashin hankali.’’
Na’ibi ya sake jawo takaddama a masallacin
A ranar juma’ar da ta gabata ma wani abu mai kamar al’mara ya faru a wannan masallacin unguwar Markaz a Agege, Legas, a daidai lokacin da mataimakin limamin masallacin ya yi yunƙurin ba da sallar juma’a, inda ya sanya shi ba da umarnin a yi kiran sallah tun kafin ƙarasowar liman, ya kuma ɗare bisa munbari ɗauke da huɗubar sa a hannunsa.
A cewar wani matashi wanda ya shaida faruwar lamarin mai suna Muhammadu Tukur, lamarin ya faru ne a lokacin sallar juma’ar ta farko da ake yi a masallacin. “Bayanda na’ibin limamin ya sanya a yi kiran sallah ne sai wani matashi ya zabura ya yi waje domin ya tabattar limamin baya nan ne, ko da matashin ya gano cewa limamin na nan sai ya dawo masallacin cikin hanzari ya katse na’urar amsakuwar da ake kiran sallah da ita, ya kuma nufi munbarin liman ya ce wa na’ibin ya sauko, ko da ya ƙi sai ya yi wuf ya wawure shi ya yi sama da shi yana ƙoƙarin fitar da shi daga masallacin,” inji shi.
Malam Adamu Abdurazak shi ne matashin da ya hana a fitar da na’ibin daga masallacin, ya shaida wa Aminiya cewa matashin da ya sungumi na’ibin limamin ya yi niyyar fitar da shi ne ɗungurungum daga masallacin sai ya yi bakin ƙoƙarinsa don ganin ba a fitar da shi ba, sannan ya bada shawarar a bar shi ya zauna wajan zamansa domin ya samu yin sallar juma’ar kamar kowa.