Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Birnin Tarayya ta yanke a kan Maryam Sanda bayan an tuhume ta da kashe mijinta.
Alkalan Kotun uku ne suka ayyana wannan hukunci ranar Juma’a bayan sun yi watsi da daukaka karar da Maryam ta yi.
- Zaben cike gurbi: ’Yan bindiga sun kawo hargitsi a Zamfara
- Buhari ya yi alhinin mutuwar Janar Domkat Bali
A watan Janairu ne dai aka tuhume ta da kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda da ne a wajen tsohon minista kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Haliru Bello.
Sai dai lauyoyinta sun tabbatar wa da Aminiya cewa za su daukaka kara zuwa Kotun Koli.
Maryam Sanda, wacce babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta yanke mata hukuncin kisa saboda zargin laifn kashe mijinta, ta daukaka kara don neman kotun ta janye hukuncin kisan da aka yanke mata.
Mai shari’a Yusuf Halilu ne ya yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 27 ga watan Janairun 2020
A cikin takardar daukaka karar da ta gabatar wadda manyan lauyoyi ke jagoranta cikinsu akwai Rickey Tarfa, SAN.
A cikin takardar an bayyana cewa, hukuncin da aka yanke mata ya tauye mata ‘yanci, musamman yadda aka gudanar da sauraron karar da abin da ya same ta sakamakon dogaro da hujjoji duk da irin shakkun da aka bayar ta hanyar shaidu, da kuma rashin bayanan sirri.