✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maryam Baba Mohammed: Jaruma a gida, jaruma a waje

Maryam Baba Mohammed na da himmar ayyukan sa-kai a bangarori da dama

A shekarar 2021, Maryam Baba Mohammed ta samu lambar yabo ta “Unsung Hero” ta Daily Trust (lambar yabon da ake bai wa mutanen da suka yi abin a yaba a tsakanin al’umma amma ba kowa ya san su ba).

Mai yiwuwa al’ummar Najeriya sun zabe ta ne saboda ayyukan da ta dade tana yi don ci gaban al’umma ba tare da ta shiga kafofin yada labarai tana sanarwa ba.

Haka kuma gidan talabijin na China, CGTN, ya taba ba ta lambar yabo ta “Pathfinder”.

Irin kalubalen da Tauraruwar tamu ta fuskanta a yarintarta, musamman a fagen neman ilimi, ya sa ta dade da sanin muhimmancin ilimantar da ’ya’ya mata.

Bayan haka kuma, ta lura da cewa ana yi wa mata abubuwa da dama marasa dadi, amma babu mai cewa komai.

Kungiyar WILI

Wadannan dalilai ne suka sa Maryam Baba Mohammed ta wayi gari da burin zama muryar da za ta yi Magana a madadin mata don kwato hakkinsu.

Su ne kuma suka sa ta kafa kungiyar karfafa mata su shige gaba a al’amuran al’umma (wato Women in Leadership Initiative, a Turance ko WILI a takaice).

Baya ga karfafa gwiwar mata, kungiyar tana kuma bayar da tallafi ga yaran da aka yiwa fyade ta hanyar sama musu mafaka, da ba su shawarwari, da ma tsaya musu idana abin ya kai zuwa kotu don kawato hakkinsu.

A yanzu haka dai kungiyar tana da rassa a biranen Abuja da Bauchi da Jos da Kaduna da Kano da Katsina da Sakkwato.

Sannan kuma burinta game da ilimi da kuma sha’awar ganin an farfado da al’adar karance-karance a tsakanin matasa suka sa ta bude wani dakin karantu (wato library) na al’umma a birnin Jos.

Ma’aikaciyar jinya

Maryam Baba Mohammed ta yi karatu sannan ta fara aikin jinya (wato nurse) a Abuja; a yanzu haka kuma tana karatun kwarewa da samun digiri na biyu a aikin na jinya.

Amma fa ba a bangaren jinya kawai ta takaita ba, domin ta je kasar Sudan inda ta karanci Larabci.

Tauraruwar tana kuma sha’awar karance-karance da tafiye-tafiye, abubuwa biyu da suka taimaka wajen fadada tunaninta da mahangarta a kan al’amura.

Maryam ta yi amanna cewa kowacce mace, musamman ’yar Arewa, tana da rawar da za ta iya takawa wajen ciyar da al’umma gaba.