✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Maryam al-Balushi: Matar da ke kiwon kyanwoyi 480 da karnuka 12 a gidanta

Wata mai kaunar dabbobi mai suna Maryam al-Balushi daga Muscat babban birnin kasar Oman, ta cika gidanta da kyanwoyi 480 wadanda galibi tsinto su ta…

Wata mai kaunar dabbobi mai suna Maryam al-Balushi daga Muscat babban birnin kasar Oman, ta cika gidanta da kyanwoyi 480 wadanda galibi tsinto su ta yi da kuma karnuka 12, inda a duk wata take kashe musu kudaden abinci da magunguna da suka kai Dala 8,000 (kimanin Naira miliyan uku da dubu 48).

Maryam al-Balushi mai shekara 51 wadda ta yi ritaya daga aikin gwamnati an tabbatar da ma’abuciyar son dabbobi ne a koyaushe, kuma ta fara tanadar su ne tun a shekarar 2008 lokacin da wani danta ya kawo wata kyanwa cikin gidansu, daga wannan lokaci ne ta fara nuna sha’awarta musamman lokacin da dan ya gaza kula da kyanwar.

Zuwa wani lokaci Maryam ta fara taimakon kyanwar da kula da rayuwarta inda a shekarar 2011, Maryam al-Balushi ta shiga cikin kunci wanda har ta kai ga ciwo bashi don taimakon ’ya’yan kyanwar.

Bayan wancan shekarar sai ta sadaukar da rayuwarta wajen taimakon tsintattun kyanwoyi tana samar musu da muhalli a gidanta.

Maryam al-Balushi tare da karnuka da kyawoyi

“Na fara sha’awar adana dabbobi a gidana ne a shekarar 2008 tun lokacin da dana ya kawo wata kyanwa gidan” Maryam ta bayyana wa kafar labarai ta AFP.

“Kamar yadda wadansu iyaye mata za ku ga abin da ’ya’yansu ke so, ba shi suke so ba, wani lokacin ’ya’yan na sha’awar kiwon dabbobi amma ba su iya kula da lafiyarsu.

Amma daga lokacin da dana ya kawo kyanwar gida, na fara sha’awar kula da ita, ina ciyar da ita abinci, in yi mata wanka sannan ina daukar lokaci tare da ita,” inji ta.

A lokacin da Maryam ta fara samar wa tsintattun kyanwoyin muhalli ta fara ne da namiji da mace, kuma  zuwa wani karamin lokaci sai ga shi ta mallaki kyanwoyi 23.

Duk da haka ta ci gaba da samar wa tsintattun kyanwoyin muhalli da hakan ya sa take zaune tare da kusan kyanwoyi 500 a gida daya.

“Allah Ya bai wa dan Adam hankalin da zai iya tunani da harcen da zai iya magana idan ba ya da lafiya don ya nemi magani, idan yana jin yunwa ya tambayi abinci amma dabba ba ta iya magana sai dai ta yi shiru, koda kuwa tana cikin tsanani,” inji Maryam.

“Jami’an gwamnati da hukumomi da wasu cibiyoyi da kungiyoyi suna iya ba da tallafi ga jama’a, amma ba a iya taimakon talakawan dabbobi da suke da bukata, sannan babu wata murya da take kira a taimaka wa dabbobin musamman tsintattu, hakan ya fi kamari a kasashen Larabawa,” inji ta.

Maryam ta mallaki gida ne a shekarar 2014 bayan suka da ta yi ta sha, kuma hakan ya sa ta samar wa kyanwoyin muhalli.

Sakamakon kula da kyanwoyi da karnuka kusan 500 yanzu Maryam na samu tallafi daga masu sha’awar wadannan dabbobi.

Maryam al-Balushi ta kasance cikin farin ciki duk da kudin da take kashe wa dabbobin.

Sakon Maryam al-Balushi ga jama’a shi ne “Jama’a su rungumi sha’awar dabbobi su kula da lafiyarsu yadda ya dace.”

%d bloggers like this: