A ranar Juma’a, 18 ga watan Agusta, an buga wani tarihi a shafi na 19, na Jaridar Aminiya mai taken :Tarihin Masarautar Lere, wanda Isiyaku Muhammed ya nakalto daga littafin Lere Chronicle, wanda Abdullahi Muhammed Doki da Ismaila Umaru Lere suka wallafa.
Tarihin ya nuna cewa mawallafan suna da ilimin tarihi musamman yadda suka nuna a cikin rubutun, sannan kuma tarihin ya kayatu.
Amma sai dai, tarihin na kunshe da kura-kurai da juya gaskiya da karin gishiri a miya domin siyasa, musamman a daidai wannan lokacin da muke ciki.
Kuskuren farko a cikin tarihin shi ne yadda aka kwakwulo asalin tarihin Lere, aka danganta su da Sanhaja na Moroko a karni na 8. Idan har haka ne, ya zama ke nan an bibbiyi tarihin har na tsawon karnuka 13 a jere har zuwa yanzu, wanda kuma yake yin hakan na da matukar wahalar gaske a irin wannan zamani da muke ciki, kamar yadda Farfesa Abdullahi Smith a kasidarsa mai taken: THE LEGEND OF THE SELFUWA: A STUDY IN THE ORIGIN OF A TRADITION OF ORIGIN, a cikin littafin tarihin tarihin Borno kafin zuwa turawan mulkin mallaka, wanda Bala Usman da Nur Alkali suka gyara kuma suka hada, shafi na 16-17 da kuma karin bayani da ke kasa a shafi na 54 ya nuna.
Hakanan kuma a cikin tarihin, Lere sun kira Sanhaja Larabawa, wanda kuma mutanen Tuareg ne ko kuma Berbers kamar yadda Ibn Kaldun ya bayyana a tarihin Maghrib na Jamif M. da Abun-Nasir shafi na 92 da kuma AL Bakri a littafinsa na al Maghrib. Wadanda ake kira da Massufa kuma dangin Sanhaja ne, kuma sauran dangoginsu su ne Lamtuna da Guddala.
Kasancewar Sanhaja Makiyaya ne, suna zaune ne a yankin Sahara daga Mauritania, ta Gabashin Sudan. Wadanda suke tare da Sanhaja su ne Zaneta da Masmuda ( a la Ibn Kaldum)
A farkon tarihin, ga duk mai tunani zai shiga rudani wajen fahimtar ma’anar Lere, inda aka ce yana nufin mazauni na dindindin a Fulatanci. Wannan na nufin cewa ya kamata suma mutanen Habe da sauran kabilun da suka zauna a wajen da Lerawa suke kira “dindindin” a ambace da girmamawa na musamman. Sai dai kuwa idan Lerewa da zuriyarsu suna so su yi amfani da tsarin Hitler na 1930 ko kuma tsarin Boer da ya haifar da rikicin nuna wariyar launi a Afirka ta Kudu, kamar yadda W. M MacMilans ya bayyana a makalarsa ta South Limpopo, shafi na 93, a littafin in the dawn of Africa history, wanda Roland Oliber ya gyara kuma ya hada.
Hakanan kuma, ya kamata ace duk Fulanin da ke zauna a tsaunukan Adamawa da sauransu da duk ana kiransu da Lere ne.
Tun daga karni na 8, sai a karni na 16, inda suka taka “Muhimmiyar rawa” wajen taimakawa Askia Muhammed na kafa daular Songhai (1492-1528). Ba Askiya Muhammed bane ya kafa Songhai, amma sai dai a zamaninsa ne daular ta samu daukaka. Wanda ya kafa daular Songhai shi ne Sonni Ali, wanda ake wa lakabi da (Ali babba), kuma ana kiransa Suleyman a tsakanin 1464-1492.
Sannan tun bayan da Lere suka taka “muhimmiyar raya” wajen kafa Songhai kamar yadda suke ce, sai a karni na 19 a lokacin jihadin Shehu Usman dan Fodio a karni na 19 (1804). Wani abin da kuma suka ce sun taka muhimmiyar rawa shi ne yadda suka dunkule a cikin Bauchi a 1908. Masu karatu za su yarda da ni cewa akwai rudani a nan. Domin kuwa sun rubuta cewa sun tare ne a wajen da suke a yanzu a shekarar 1790 kamar suka rubuta a Aminiya, amma kuma sun rubuta cewa sun tare ne a shekarar 1173 a wani takarda mai taken: Lere Progressibe na 10 ga watan Oktoba, shekarar 1980. Sannan kuma jihadin Sakkwato a shekarar 1804 da na Bauchi a shekarar 1808 sun yi kusa saosai, da zai yi wuya ace Lere sun halarci duka.
Kuma babu wani fassara da za ayi wa sakin layi na 8 da na 9 na tarihin da aka face ace Lerawa suna janyo wa Yakubu (wanda ba su fada cikakken sunansa ba) rigima, tun da sun ba shi sarautar sarkin Yaki. Wasu masu sarautun gargajiya a Bauchi suna rike da wannan sarauta har zuwa yau, misali, Ajiyan Bauchi da Hakimin Lere, suna cikin manyan ‘yan majalisar sarki. Me ya sa Lere (Maudu’inmu) suka bar na su, suka koma suna hadewa da Zazzau a matsayin karamar masarauta (bassal state), inda Zazzau ta mayar da su matsayin Dagaci?
A maganar tarewa a wajen da suke a yanzu (1773 ko 1790) kuwa, lokacin sarakunan Habe ne ke rike da Zazzau. A shakarar 1773, sarkin Zazzau Cikkoku ne (1773-1779, kuma 1790, lokacin Jatau dan Isiyaku ne ke sarauta (1782-1802). Wadannan sarakunan Haben, sune na 57 da 59 a cikin sarakunan Habe 60 da aka yi a masarautar Zazzau kamar yadda Usman dalhatu na bayyana a littafinsa na Malam Ja’afaru dan Isiyaku babban Sarki, shafi na 542. Don haka wannan shi ya sa na ce danganta abubuwan da suka wakana a Sakkwato (1804) da Bauchi (1808) ba zai yiwu ba.
Su Kurama sun yi amanna (ko dai daidai ne ko ba daidai ba) cewa zuriyar Lere bangaren mutane Sayawa ne, wadanda suka taso daga Leren Bauchi. Suna da dangantakar auratayya da Kurama ta hanyar Sanhaja tun karnuka 13 da suka wuce (shekaru 1300), amma ba da Kurama ba, a shekarar 200 da suka wuce.
Shin zai yiwu ace Lere sun gano asalinsu fiye da shekara 200, amma kuma ba su bayyana wasu daga cikin makwabtansu? Duk kuwa da cewa suna makwabtaka da Kurama, Kahugu, Gure, Amawa, Surubu, Kono, Kaibi ko Dingi da sauransu. Babu kabilar da aka ambata a sakin layi na 26 na tarihin Lere da aka wallafa a Aminiya, anya wannan na nuna “zaman arziki”
A bangaren sanya siyasa a cikin wannan tarihi kuwa, ya kamata ku lura da yanayin da siyasar Jihar Kaduna ke ciki a a yanzu. Wuraren da aka assasa domin su samar da cigaba da zaman lafiya a tsakanin mutane, duk an cire su. Wannan ne tarihin Leren da aka wallafa a Aminiya ya so ya ci moriya.
Amma ko ma mene ne, Kurama a matsayinta na kabilar da ta fi kowace kabila girma a Kudu maso Gabshin Zazzau kamar yadda H.D Gunna ya bayyana, suna nanata cewa :
a. Yankin na da girma kuma ta hada mutane dabam dabam
b. Yiwuwar wata kabila ta danne wata zai hana zaman lafiya (Kurama sun yi rubuce-rubuce da dama a kan wannan matsayar)
c. Dub abin da ke da kyau ga wata kabila, to ya kamata ya zama yana da kyau sauran kabilun.
A karshe, muna karni na 21 ne, don haka ya kamata ne mu hada hannu wajen fahimtar juna da fahimtar bambancin da ke tsakaninmu a matsayinmu na makwabta, sannan kuma ya kamata mu rika girmama kowace kabila.