✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marin da na yi maka daga hannuna ne ko daga kumatunka?

Wani mashayi ne ya fito daga wurin shaye-shayensa sai ya iso wani wurin wa’azi da isarsa sai ya fara gardama da ’yan agaji kan su…

Wani mashayi ne ya fito daga wurin shaye-shayensa sai ya iso wani wurin wa’azi da isarsa sai ya fara gardama da ’yan agaji kan su bari ya shiga. Sai malamin ya ce su bari ya shigo watakila ya zo neman fatawa ce. Aka bari ya shiga sai ya ce Malam ina da tambaya,ya ce idan ana nika gyada ina jin wani irin kuka daga cikin injin. To Malam kukan daga injin ne ko daga gyadar ce?
Ashe akwai mahaukaci a kusa, sai kawai ya taso ya kashe mashayin nan da mari ya ce marin da na yi maka daga hannuna ne ko daga kumatunka ne?
Daga 09099886988