A ranar 2 ga watan Satumbar 2017 ne Allah Ya karbi ran Dokta Hafiz Suleiman Wali, kwararren malami kuma masani a harkar ilimi. Marigayin shi ne ya kirkiro da Kwalejin Horar da Malamai (NTI) da ke Kaduna. Marigayin ya rasu ne a babban Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano a lokacin yana da shekara 81, bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Marigayi Wali, ya kasance malami ne a daukacin rayuwarsa da hakan ta sa ya karfafa batun a rika bayar da ilimi ko daga nesa ne (distance learning) da hakan ta sa ya bayar da shawara wajen kirkiro da Kwalejin Horar da Malamai ta Kaduna (NTI).
Ya fara harkar koyarwa ne a Sakandaren Yerwa da ke Maiduguri daga baya ne aka yi masa canjin wurin aiki zuwa Kwalejin Horar da Sana’o’i ta Idah da yanzu take karkashin Jihar Kogi. Daga nan ya koma Kwalejin Horar da Sana’o’in hannu ta Mashi da ke Katsina. Ya kuma taba koyarwa a Kwalejin horar da sana’o’i ta Wudil kafin a yi masa karin girma zuwa mukamin Insifekta a Jihar Kaduna.
Marigayin ya taba aiki da kungiyar kasashe rainon Ingila a matsayin aro amma daga baya suka mayar da shi ma’aikacinsu na dindindin. Sannan ya taba yin aiki a kasar Kanada har na tsawon shekaru 2 daga nan ne ya koma Najeriya.
Bayan ya yi ritaya ne sai ya shiga harkar samar da bayanai da sadarwa irin na zamani (Information and Communication Technology, ICT). Ya zama mai bayar da shawara kuma abin tuntuba na kashin kansa a bangaren harkar ilimi da kuma ta sadarwa irin ta zamani.
Daga cikin manyan mutanen da marigayin ya taba yin karatu da su a Kwalejin Barewa ta Zariya sun hada da Tsohon Shugaban kasa Yakubu Gowon da Marigayi Janar Hassan Usman Katsina da Marigayi Sarkin Lere Alhaji Umaru Lere da Dokta Rilwanu Lukman da Alhaji Umaru Dikko da tsohon Gwamnan Arewa maso Yamma Alhaji Usman Faruk da Alhaji Abdullahi Yusuf Yero da sauransu.
A lokacin da yake koyarwa a Kwalejin Koyar Sana’a ta Mashi da ke Jihar Katsina ce ya samu yabo daga Firimiyar Jihar Arewa Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato saboda kwazonsa. Ya samu yabon ne bayan daliban da ya horar suka gina wasu ajujuwa da kuma dakunan dalibai a harabar kwalejin a matakan horar da su. A kan haka ne Amurka ta ba shi gurbin yin karatun Digiri na biyu a karkashin tallafin da Cibiyar Ford Foundation ta bayar inda ya yi karatu a fannin injiniya.
Hafiz Wali ya fito ne daga zuri’ar Wali masu rike da sarautar Wali a Kano. Sarautar Wali dai ana ba wadanda ba su da gadon sarauta ne a Kano kuma an kirkiro ta ne saboda masu ilimin addini da na zamani wadanda ke da alhakin ba Sarkin Kano shawara a kan harkokin shari’a.
Don haka ba a yi mamaki ba a lokacin da marigayi Hafiz Wali ya kasance shugaban Kwamitin Duban Wata na kasa (National Moon Sighting Committee) kuma kwamitin yana karkashin Majalisar Malaman Addinin Musulunci ta kasa ne (Nigerian Supreme Council for Islamic Affairs) da ke karkashin shugabancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar.
Yadda kwamitin ganin wata yake gudanar da ayyukansa musamman a lokacin watan Ramadan ya taimaka wajen rage matsalolin da ke tattare da ganin wata a Najeriya.
Marigayi Hafiza Wali mutum ne da ake girmama shi saboda iliminsa, kuma Allah Ya yi shi mai saukin kai da kuma tsage gaskiya. An shaide shi da kaifi daya, kuma mutum ne da ke jajircewa a kan fadin gaskiya da aiki da ita a kowane lokaci.. Jama’a da dama sun yaba da yadda wannan bawan Allah ya gudanar da rayuwarsa musamman a bangaren bayar da ilimi da kuma taimakon al’umma.
Babban burinsa shi ne ya horar da ’yan Najeriya a bangaren aikin injiniya da hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma samar da ayyukan yi. A wata hira da jaridar Turanci ta Daily Trust ta taba yi da shi ya ce :”a lokacin da nake shugaban wata Kwaleji (Principal) na hore su da su yi kokarin yin karatu a fannin injiniya don hakan zai amfane su a daukacin rayuwarsu. Yanzu dai maganarsa ta tabbata ganin yadda babu bangaren da ba a bukatar wadanda suka yi karatu a bangaren injiniya misali a bangaren gine-gine da kare-kere da bangaren kwamfuta da na wutar lantarki da sauransu. Misali a yanzu, babu wani abu da za a aiwatar cikin sauki ba tare da an yi amfani da na’ura mai kwakwalwa ba.
Hafiz Wali ya yi rayuwa mai inganci kuma ko shakka babu iyalansa da abokai da ’yan uwa da daukacin al’ummar kasar nan za su yi rashinsa.
Muna yi masa addu’ar Allah Ya jikansa da Rahama, kuma Allah Ya albarkaci zuri’arsa.