Babu shakka, shirin nan na sanya fitila mai aiki da hasken rana ‘Solar’ da Gwamnatin Tarayya ta yi a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi abu ne mai matukar faranta zuciya.
Sannan shirin zai zamo alheri ga daukacin ’yan kasuwar ta Sabon Garin Kano bisa la’akari da canjin zamani da ake samu, musamman lamarin da ya kunshi hasken wutar lantarki da yadda wutar lantarki take karanci a wannan kasa tamu.
Kasuwar Sabon Garin Kano, kasuwa ce wadda Allah Madaukakin Sarki Ya yi wa albarka a harkokin kasuwanci, sannan ta yi fice sosai wajen samar da wani babban kaso ga tattalin arzikin wannan kasa, musamman a sha’anin kasuwancin zamani tun lokaci mai tsawo.
Bugu da kari, kasuwar ta Sabon Garin Kano ta jima tana fama da matsalar gobara, inda a baya-bayan nan aka samu wani babban bala’i, inda kuma ya yi sanadiyyar asarar dukiya mai yawa, sannan ’yan kasuwa kanana masu yawa suka rasa jarinsu, kuma tilas suka hakura da kasuwancin.
A wannan lokaci sai ga shi Gwamnatin Tarayya ta yi tunani mai kyau na samar da wutar lantarki mai amfai da hasken rana domin haskaka kasuwar. Kuma ita wannan wutar lantarki mai amfani da hasken rana ba ta cika haddasa gobara ba, domin yanzu duniya tana kara sauya samfurin samar da wutar lantarki zuwa mai aiki da rana kuma tuni kasashe suka kasance cikin wannan tsari.
Bisa haka ne nake kara nanata cewa wannan tsari da ya zo Kasuwar Sabon Gari yana da kyau kuma ya zo a daidai lokacin da ake bukatarsa, illa kawai mu ba da goyon baya ga wannan kokari na Gwamnatin Tarayya.
Sannan muna mika godiya ta musamman ga Gwamnatin Jihar Kano, saboda kyautata yanayin kasuwanni da take yi domin bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya kamar yadda aka san Jihar Kano da su.
A karshe, ina fatan alheri ga Kwamishinan Kasuwanci na Jihar Kano Alhaji Ahmad Rabi’u da Shugaban Hukumar Kasuwar Sabon Gari, Alhaji Sani Abdullahi kofar Mata da daukacn ’yan Kasuwar Sabon Garin Kano saboda haduwa da aka yi wajen inganta yanayin kasuwanci a kasuwar.
Alhaji Ado Bilyaminu, shi ne Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwar Sabon Garin Kano (AMATA), 08063801898. medialink57 [email protected].