✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marayu 200 sun samu tallafin N50,000 kowannensu a Yobe

An zai marayun ne daga Kananan Hukumomin Jihar 17

Marayu 200 a Jihar Yobe sun samu tallafin N50,000 kowannensu domin fara sana’o’i.

Gwamna Mai Mala Buni na Jihar ne ya tallafa wa marayu 200 da aka zabo daga Kananan Hukumomi 17 na jihar da N50,000 kowanne.

Gwamna Buni ya ce an yi hakan ne domin a taimaka wa marayun da jari don fara sana’o’i da kuma dogaro da kai a matakin farko na rayuwa.

“Fatanmu ne cewa wannan taimakon zai kara amfani ga rayuwarku da makomarku,” inji Gwamnan.

Marayun wadanda shekarun su ke tsakanin shekaru tara zuwa 14 sun fito ne daga  Kananan Hukumomi 17 na Jihar.

Ustaz Babagana Malam Kyari, Kodinetan shirin kuma mai ba Gwamna Buni shawara kan harkokin addini, ya ce wannan shi ne karon farko da ake tallafawa marayu da yawa a Jihar kamar haka.

Ya ce matakin da Gwamnan ya yi zai rage barazanar barace-barace a kan tituna musamman marayun da ba su da sana’a.

Malam Kyari ya yi kira ga masu kula da marayun da su tallafa musu tare da tabbatar da yin amfani da abin da suka samu ta bin hanyoyin da suka dace.