Diego Armando Maradona ya shawarci Lionel Messi ya hakura da buga wa kasar Ajantina kwallo ganin ya fara tsufa.
Messi mai shekara 31, rabon da ya buga wa Ajantina wasa, tun bayan da aka kammala gasar cin Kofin Duniya a Rasha.
Hasali ma dan kwallon ba ya cikin ’yan kwallon Ajantina da za su buga wa kasar wasannin sada zumunta da kasashen Brazil da Iraki a wannan mako.
Rahotanni sun ce da wuya dan kwallon ya sake yi wa Ajantina kwallo, ganin a baya ya taba shaida wa duniya cewa ya daina buga wa kasar kwallo, amma mahukunta Ajantina suka lallashe shi ya koma ruwa saboda gasar cin Kofin Duniya ta bana.
Ganin bai tabuka abin kirki a gasar cin Kofin Duniya ba ya sa har yanzu bai sake yi wa kasar kwallo ba. Wannan wata alama ce da ke nuna Messi yana kokarin jefar da kwallon mangwaro ne don ya huta da kuda.