Sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi wanda aka yi wa lakabin Sarki Muhammadu Sanusi na II, ya samu shiga fadar Kano, ya kuma dare kan karagar mulki kamar yadda Allah Ya zabi magabatansa a gidan Dabo, bayan da Sakataren gwmanatin jihar Kano Alhaji Rabi`u Sulaiman Bichi a ranar Lahadin wancan makon 8-06-2014, ya bada sanarwar nadinsa, bisa ga amincewar da gwamnan jihar Injiniya Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso ya yi masa daga cikinsunayen mutane uku da masu zaben sabon Sarki na Masarautar Kano suka mika masa. Wadanda aka mika sunayen nasu don gwamnan jihar ya zabi daya daga cikinsu ya kuma tabbatar masa da karagar magabatansa, sun hada da Alhaji Sanusi Lamido Ado Bayero, Ciroman Kano, kuma babban dan marigayi Sarki Ado Bayero, sai mai girma Wamban Kano Alhaji Abbas Sanusi, dan Sarki Sa Muhammadu Sanusi da ya mulki Kano tsakanin shekarar 1954, zuwa ta 1963, sai shi kuma Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, wanda jika ne ga Sarki Sa Muhammadu Sanusi.
Ba aniyar makalar ta yau ba ce, wadda na yi alkawarin kawowa a wannan makon, ta mayar da hankali akan cikakken tarihin sabon Sarki Malam Muhumamadu Sanusi na II, ba, amma ina ga babu laifi idan na yi kokarin kawo dan wani abu daga cikin tarihinsa. An haifi sabon Sarkin a cikin birnin Kano a ranar 31-07-61, ya yi karatunsa na Sakandare a Kwalejin Kings da ke Legas, inda ya zarce Jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya yi digirinsa na farko a fannin tattalin arziki, Jami`ar da bayan ya kammalata ya kuma yi aikin koyarwa a cikinta, har na tsawon shekaru biyu, ya kuma yin wani digirin a fannin shari`ar Islama a Jami`ar Afirka da ke birnin Khartourm na kasar Sudan.
A shekarar 1985, Sarki Muhammadu Sanusi na II, ya fara aikin Banki, aikin da shi ya shara da Bankin Icon a shekarar 1997, ya kom aiki da Bankin UBA, har zuwa shekarar 2005, lokacin da likkafa ta yi gaba ya zama Darakta mai cikakken iko na Bankin First Bank, inda daga bisani ya zama Manajin Darakta, wato Oga kwata-kwata kuma dan arewa na farko a cikin tarihin Bankin na sama da shekaru 100, da kafuwa a kasar nan a shekarar 2009. Yana kan wannan mukami ne kusan watanni shidda, sai likafa ta yi gaba, shugaban kasa marigayi Umaru Musa `Yar`aduwa ya nada shi Gwamnan Babban Bankin kasar nan, a ranar 03-06-2009, mikamin da yake rike da shi har zuwa cikin watan Fabrairun bana da ya fallasa bacewar wasu makudan kudin man fetur daga Kamfanin man fetur na kasa, har Dalar Amurka biliyan 20, fallasawar da bata yi wa shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan dadi ba, don haka ya dakatar da shi daga kan mukaminsa, wanda koda haka ba ta faru ba, dama wa`adinsa na zangon farko na shekaru biyar zai kare a ranar 3 ga wannan watan na Yuni .
A zaman sa na Gwamnan babban Banki, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi kamar yadda ake kiransa a wancan lokaci, ya fuskanci babban kalubale a farkon hawansa, bisa ga kasancewar a lokacin tattalin arzikin duniya baki daya yana fuskantar rugujewa, al`amari da mu ma ya shafe mu, musamman a cikin tafiyar da bankunanmu. Don haka ya kawo manya-manyan canje-canje, tare da bankado almundahana ta wawure kudin masu ajiya a bankuna da wasu shugabanni da Daraktocin wasu Bankunan suka yi, binciken da ya kai aka daure tare da kwace dukiyoyi da kaddarorin irin wadancan shugabanni da `yan koransu da suka rinka hada kai da su suna kwashe kudin jama`a.
A takaice, aikin da ya yi a Babban Banki, shi ya haska shi kasa da duniya baki daya ta san cewa shi jajircacce ne, kuma ba ya jin tsoron ya yi ko ya fadi albarkacin bakinsa akan dukkan wani abu da ya tabbatar da ba daidai ba ne.
Bayan bayyana nadinsa an samu zanga-zanga ta kusan kwanaki biyu daga wasu da suke kallon tamfar Allah ba zai iya ba shi wannan mukami ba, wannan kuma yana cikin tarihi na ita kanta masarautar ta Kano da wasu masarautu na Daular Shehu Usman dan Fofiyo (RA). Alal misali a lokacin da Turawa suka nada Marigayi Sarkin Musulmi Abubakar a zaman Sarkin musulmi a shekarar 1938, tarihi ya tabbatar sai da ya samu wasu kwanaki masu yawa yana barikin sojoji, bisa bore da aka yi wa nadinsa, amma sai ga shi yau shekaru 26, da rasuwarsa kusan a kullum ana begen ayyukan alkherin da ya yi. Haka labarin yake a lokacin da aka nada mai alfarma Alhaji Ibrahim Dasuki da ya gaje shi a shekarar 1988.
Shi kansa marigayi Sarki Alhaji Ado Bayero, da aka nada shi a shekarar 1963, ya fuskanci irin wannan boren, amma kuma ga shi ya mutu an yi bore akan nadin wanda ya gaje shi. Kusan ya zama al`ada ga talakawa, su tausaya wa duk iyalen Sarkin da ya mutu muddin ba a bar sarautar a gidansa ba. Wannan tausayawa ce ta dan Adam, amma ga `yan sarauta, sarauta ta fita daga wannan gida zuwa wancan ba wani sabon labari ba ne, shi ya sa ka kan ji sukan ce ai Sarauta ta mai rabo ce ga `ya`yan Sarki.
Yanzu dai cikin yardar Allah da iyawarSa da ikonSa, Alhaji Sanusi Lamido Sanusi ya zama magajin Dabo na 14, nasara ko rashin nasarar zamaninsa za su dogara ne kacokan akan yadda ya iya tafiyar da mulkinsa, kodayake masu iya magana kan ce“Ba a mugun Sarki sai mugun Bafade”, amma duk da haka yanzu ya zama wajibi ga sabon Sarki ya kwan da sanin cewa yawan maganganu akan al`amurran kasar nan yanzu za su takaita gare shi, wato dole ya rinka jan Amawali. Akwai kuma batun yadda zai zauna da kungiyoyin addinai da na dariku, musamman bisa zargin da aka fara yi masa na cewa shi dan Shi`a ne duk kuwa da irin yadda mutanen da suka san shi tun yana cikin gwagwarmayar kungiyar dalibai Musulmi a zaman dalibi, da bayan ya kama aiki.
Mutane irinsu Farfesa Umar Labdo, shugaban fannin kimiyar dan Adam Jami`ar Arewa maso yamma, mallakar Gwamanatin Jihar Kano, wanda suka yi waccan gwagwarmaya da sabon Sarkin ya tabbatar da cewa bai san shi ba batun Shi`a ba, dadin dadawa kuma hutubar sallar Juma`ar farko da sabon Sarkin ya shugabanta a juma`ar da ta gabata ta tabbatar da cewa shi ba dan Shi`a ba ne, bisa ga irin sakon da ta kunsa.
A kan harkokin gudanarwa na fada, na san sabon Sarkin ya san cewa wani wuri ne inda kwarya ke bin kwarya, amma kuma wani lokacin wanda kake ganin bai isa ba, shi zai isa kuma haka din za a yi. Ba na jin ko kusa sabon Sarki zai samu wata matsala, don ko ba kome ga babban Malaminsa, wanda ke rike da sarauta a masarautar ta Kano tun a shekarar 1958, a zaman Hakimi, wato Alhaji Abbas Sanusi, wanda kuma uba yake ga sabon Sarkin, kasancewarsa kane ga marigayi Ambasada Aminu Sanusi, wanda shi ne mahaifin sabon Sarki Muhammadu Sanusi na II. Don haka Allah Ya kama, Ya ja zamanin Sarki!
Maraba da Sarki Muhammadu Sanusi na II
Sabon Sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi wanda aka yi wa lakabin Sarki Muhammadu Sanusi na II, ya samu shiga fadar Kano, ya kuma dare…