✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maraba da Manzon Allah (3)

Duniya tana ciki tsananin bukatar mai ceto, amma ga alama babu wani a kusa da zai iya fitar da ita daga wadannan duffai. Babu wani…

Duniya tana ciki tsananin bukatar mai ceto, amma ga alama babu wani a kusa da zai iya fitar da ita daga wadannan duffai. Babu wani addini, babu wata manufa, babu wata akida babu wata koyarwa da za ta kawo wa dan Adam saukin wadannan bala’o’i da musgunawa. Babu wani addini a lokacin da yake da alama ta kasancewa na duniya, ko ya nuna shi ba na wani yankin kasa ba ne ko na wasu kebabbun al’umma ba. Babu wani addini da yake yin wa’azi ko karantarwa domin yaki da nuna fiffiko ko nuna wata kabila ta fi wata daraja a lokacin.
Wannan shi ne halin rudu da duniya ke ciki, inda Allah Madaukaki Ya zabe ka ya Manzon Allah! Ya ba ka Risala ta karshe a matsayin cikakamakin Annabawa kuma Shugaban Manzanni, Ya aiko ka da sakon Musulunci wato sakon mika wuya ga Allah Mahalicci zuwa ga dukkan duniya, domin ka fitar da mutane daga duffan kafirci da zalunci da almundahana da jahilci da tabarbarewar tarbiyya da suka dabaibaye duniya suke neman halaka mutane, zuwa ga hasken imani da adalci da amana da ilimi da dabi’u nagari.
Ya Ma’aikin Allah! Lokacin da aka aiko ka, ba ka yi kira don fifita wata kabila ko wani jinsin mutane a kan wani ba, a’a ka tsaya ne don ceto daukacin mutanen duniya ba tare da lura da bambancin kabila ko launin fata ko aji ko mukami ko harshe ko yankin kasa ba. Sakonka sako ne na duniya baki daya, sako ne na kokarin kawar da duk wani fasadi da zalunci da musgunawa da dan Adam ke fuskanta. Sakonka cikakke ne ya shafi ibada da mu’amala da zamantakewa da tattalin arziki da diplomasiyya da yaki da sulhu da komai. Sako ne da ba kawai ya kawo Juyin Juya-Hali a zamanin da ka zo da shi ba ne, ko yau haskensa bai dushe ba yana ci gaba da haskaka wa masana ba na Musulmi kadai ba na dukkan fagagen ilimi da rayuwar dan Adam.
Domin haka daga lokacin da mutanen zamani suka amince su yi watsi da akidar jiji da kai da alfahari za su fahimci hakikanin gaskiyar abin da ake kira MUSULUNCI da ka zo da shi da kuma kai Annabin karshe MUHAMMAD (SAW). Za su fahimci cewa kai da sakonka ba kun kebanta ko kun shafi Larabawan karni na 14 kawai ba ne, za su fahimci cewa kai da sakonka za ku taimaka wajen warware hardaddun matsalolin zamaninmu, Zamanin Zuwa Sararin Samaniya! Zamanin kere-kere da ci gaba, Zamanin… Zamanin…
Za su fahimci cewa Musulunci ba addini ne da aka jingina shi ga wani Annabi ba, kamar Masihiyya (Christianity) da ake jingina shi ga Annabi Isa Almasihu ko Yesu Kiristi. Kuma ba addini ne da ake jingina shi ga wani waliyyi ba kamar yadda ake jingina addinin Buddah da waliyi Buddah, kuma ba addini ne da ake jingina shi ga wata kabila ba, kamar yadda ake jingina addinin Yahudanci ga kabilar Yahudawa a yau (Judanism), kuma ba addini ne da ake jingina shi ga wani sarki ko mutum ba. Musulunci na nufin mika wuya ga Allah Mahaliccin duniya da abin da ke cikinta, Wanda Ya kagi halittar mutum kuma Ya sanya shi mafi kyawun halitta, Ya ba shi hankali da tunani, wannan addini shi ne addinin dukkan Annabawa da Manzanni (AS) tun daga Annabi Adamu (AS) har zuwa Annabi Muhammad (SAW) koda da wane irin suna mutane za su kira addinin Annabawan. Wannan mika wuya ga Allah tana ’yantar da dan Adam daga zama bita-zaizai ga sauran abin halitta, tana ’yanta shi daga bauta wa gumakan da ya sassaka da hannunsa ko ya bi ra’ayin wani masani ko dan falsafa ko gwani ko kwararre da bai halicci kansa ba balle ya halitta wani, ko ya bi wani mutum saboda karfin tsafi ko sihirinsa ko mulkinsa sabanin umarnin Ubangijinsa.
Musulunci ba kwatsam ko afke ya bayyana a duniya ba, a’a cikato ne na sakonnin Annabawan da suka gabata, da ya fara bayyana bayan dan Adam ya karkace daga tafarkin da Allah Ya dora shi a kai. Kuma domin Allah Ya kammala wannan sako Ya cika wannan addini ne Ya zabi Annabi Muhammad (Mashayabo) domin ya kasance Annabin karshe kuma shugaban dukkan Annabawan da suka gabata, wadanda dukkansu sun yi bushara da zuwansa, Annabi ne da rayuwarsa ta zama cikakkiyar abar koyi gare mu da duk wani mai son tsira.
Ya Rasulullah! Alkalamina ya yi kadan ya yi rubutu kan hakikaninka, ba zan iya rubuta wani abin kirki ba a kanka, a matsayinka na Annabin da ya kawo canji a duniya gaba dayanta. Kalmomina sun gaza wajen bayyana ko kai wane ne, lura da cewa Allah ne Ya zabe ka domin wannan gagarumin aiki Ya dora maka wannan amana kuma ka sauke ta saukewar da duniya ta shaida ka isar da sako kuma ka ba da amana. Yaya zan iya bayyana kai wane ne, bayan ta kowane gefe ka cika ka batse ta yadda hatta makiya da masu adawa da kai da masu zame maka kafa suka kasa gano wani laifi da za su iya jifar ka da shi?!
Me zan iya cewa a kan Annabin da Alkur’ani ya bayyana shi da “Abin koyi Mai kyau,” ga dukkan halitta ciki har da masu zuwa nan gaba? Tabbas ka cancanci kirarin da Allah Madaukaki Ya yi maka lokacin da Ya bayyana ka a cikin Alkur’ani da cewa: “Kuma lallai, hakika, kana a kan halayen kirki, manya.” (k:68:4)? Kuma me zan iya cewa a kanka ya Annabin Allah, alhali Allah Ya ce da kai: “Kuma ba Mu aike ka ba, face wata rahama ga talikai.” (k:21:107)?  
Ya Manzon Allah! Ka fita daban, domin Allah Ya yi maka baiwa da dukkan kyawawan halaye kamar hakuri da jarumta da hikima da kyauta da hazaka da kauna da tausayi da sauran halayen kirki, wadanda za su iya zame mana ababen koyi wajen gyara rayuwarmu. Duk da haka Ya Rasulullah! Kai bawan Allah ne kuma ManzonSa ne (SAW). Wannan siffa ce ka fi son a kira ka da ita “Bawan Allah!”