✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maraba da Manzon Allah (1)

Addu’ar Annabi Ibrahim (AS) Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugaban mutanen farko da na karshe…

Addu’ar Annabi Ibrahim (AS)

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Shugaban mutanen farko da na karshe Annabi Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar Alkiyama.
Bayan haka, yayin da muka shiga watan Rabi’ul Awwal watan haihuwar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), muna ganin ya kamata mu sake gabatar da rubutu kan wani abu daga rayuwar Manzon Allah, domin mu ce wani abu kan wannan Manzo mafi girma a cikin Manzannin Allah. Sannanne ne cewa watan Rabi’u Awwal shi ne watan haihuwar Annabi Muhammad (SAW) fitila mai haskaka duniya, Annabin da duniya ba ta taba samun irinsa ba tun daga kakanmu Annabi Adamu (AS), kuma ba za ta samun irinsa ba har zuwa ranar da za a nade kasa.
Muna yi maka maraba ya Manzon Allah a daidai lokacin da ka bar duniya da kimanin shekara 1405. Muna yi maka maraba ne saboda sakonka yana raye a tsakaninmu koda ba ka tare da mu a gangar jiki. Muna yi maka maraba ne saboda kamar yau aka haife ka, sakamakon komawar duniya ga rayuwar Jahiliyya kamar yadda ka zo ka iske ta! Muna yi maka maraba ne bisa fatar mu sake yunkuri daga inda ka fara don gyara al’amura kamar yadda ka yi. Muna yi maka maraba a daidai lokacin da muka rasa alkibla muka rude muka bar gwadaben da ka bar magabatanmu a kai! Muna yi maka maraba ya Rasulullah da fatar sunnarka za ta jagorance mu zuwa ga komawa ga irin rayuwarka.
Ya Ma’aikin Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare ka! Haihuwarka cika alkawari ne na Allah na aiko da Manzo na karshe da sakonsa zai kasance sako na karshe zuwa ga dan Adam. Bisa ga haka ka zo da Alkur’ani Mai girma domin ya zama Alkawalin karshe a bayan Tsohon Alkawali da Sabon Alkawali.
Haihuwarka ya Annabi Muhammad (SAW) a birnin Makka cika alkawarin da Allah Madaukaki Ya yi ne kan addu’ar kakanka Annabi Ibrahim (Alaihis Salam) wanda ya roki Allah Ya fitar da wani Annabi daga tsatsonsa a lokacin da shi da dansa Annabi Isma’il (AS) wanda Allah Ya umarta ya ajiye shi a garin Makka lokacin da yake daji suke yunkurin gina dakin Ka’aba. Alkur’ani Mai girma ya bayyana ganawar da ta gudana a tsakanin Annabi Ibrahim da Ubangijinsa da kuma abubuwan da suka biyo baya kamar haka:
“Kuma ka tuna, a lokacin da Ubangijin Ibrahim Ya jarrabe shi da wasu kalmomi, sai ya cika su. Ya ce: “Lallai ne Ni Mai sanya ka shugaba domin mutane ne. (Ibrahim) Ya ce: “Kuma daga zuriyata (ma Ka sanya).” Allah Ya ce: “AlkawariNa ba zai samu azzalumai ba. Kuma a lokacin da Muka sanya dakin ya zama makoma ga mutane, da aminci, kuma suka riki wurin Sallah daga Makama Ibrahim, kuma Muka yi alkawari zuwa ga Ibrahim da Isma’ila da cewa: “Ku tsarkake dakiNa domin masu dawafi da masu lizimta da masu ruku’i, masu sujada. Kuma ka tuna a lokacin da Ibrahim ya ce: “Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari (Makka) amintacce, Ka azurta mutanensa daga ’ya’yan itacen, wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira daga gare su.” Allah Ya ce: “Wanda ya kafirta ma Ina jiyar da shi dadi kadan, sa’an nan kuma Ina tilasta shi zuwa ga azabar wuta. Kuma makomar ta munana. Kuma a lokacin da Ibrahim yake daukaka harsashin gini ga dakin (shi) da Isma’ila (suna cewa:) “Ya Ubangijinmu! Ka karba daga gare mu, lallai Kai, Kai ne Mai ji Mai sani. Ya Ubangijinmu! Ka sanya mu, mu biyu wadanda suka sallama (musulutna) gare Ka, kuma daga zuriyarmu (Ka sanya) al’umma mai sallamawa zuwa gare Ka, kuma Ka nuna mana wuraren ibadar hajjinmu, kuma Ka karbi tuba a kanmu. Lallai ne Kai, Kai ne Mai karbar tuba, Mai rahama. Ya Ubangijinmu! Ka aiko a cikinsu wani manzo daga gare su, yana karanta musu ayoyinKa, kuma yana karantar da su Littafin da hikimar, kuma yana tsarkake su. Lallai ne Kai, Kai ne Mabuwayi, Mai hikima.” Kuma wane ne yake gudu daga akidar Ibrahim, face wanda ya jahilta ga ransa? Kuma lallai ne, hakika Mun zabe shi a cikin duniya, kuma lallai ne shi a cikin Lahira, hakika, yana daga salihai. A lokacin da Ubangijinsa Ya ce masa: “Ka sallama (ka musulnta),” ya ce: “Na sallama (mika wuya) ga Ubangijin talikai.” (k:2:124 – 131).
Bayan amsar wannan addu’a daga kakanka kuma kakan Annabawa Annabi Ibrahim (AS) da duk wani mai bin addinin da yake da alaka da wahayi ke tinkaho da shi, sai kuma busharar dan uwanka Annabi Isa (Yesu Almasihu) dan Maryam (AS) game da zuwanka kamar yadda ya zo a cikin Suratus Saffi inda Allah Madaukaki Yake cewa: “Kuma ka tuna a lokacin da Isa dan Maryama ya ce: “Ya Bani Isra’ila! Lallai ni, Manzon Allah ne zuwa gare ku, mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bayar da bushara da wani Manzo da ke zuwa a bayana, sunansa Ahmad (Mashayabo).” To a lokacin da ya je musu da hujjoji, sai suka ce: “Wannan sihiri ne, bayyananne.” (k:61:6).

Duniya kafin aiko ka (SAW):
Lokacin da Allah Madaukaki Ya aiko ka a matsayin ManzonSa na karshe, ya Rasulullahi! Duniya cike take da fasadi da rarrabuwa. An jirkita tare da watsi da sakonnin da Annabawan da suka gabata suka kawo. Ba wani ci gaba, sai koma baya da dan Adam ke ciki, rayuwarsa tana dada shiga duhu, babu zance wani abu wai shi imani. Zalunci da almundahana da cin hanci da rashawa ne suke cin kasuwa a ko’ina a duniya. Danniya da tauye hakkin mata da raunana sun zama abin gasa a tsakanin daulolin duniya. Duniya gaba daya tana cikin duhun da dan Adam bai taba shiga irinsa a tarihinsa ba. Wannan ne ya sa Alkur’ani Mai girma ya bayyana rayuwar da ake ciki a lokacin aiko ka da rayuwar Jahiliyya.
Ya Ma’aikin Allah! A yau bayan ka isar da sako, ka ba da amana, mutane sun yi watsi da koyarwar addini sun yi tawaye ga sakonnin Manzanni da ka zama cikamakinsu, sun bijire wa Allah sun koma ga bin son zukatansu, sun koma rayuwa irin ta Jahiliyya. Jahiliyyar da ka iske ka yi faman kawar da ita a zamaninka ta sake dawowa a bayanka, duk da cewa al’ummarka ta fi kowace al’umma ci gaba a fannin kimiyya da kere-kere har tana iya zuwa sararin samaniya ta shakata ta wala ta baje kolin wasu kayayyaki a can, kuma tana takama da na’urori iri-iri, amma wannan bai hana ta komawa ga irin zaman Jahiliyya ba, saboda ta koma ga bin son rai da sha’awarta!
Ya Rasulullah! Duk alamomin da suka hada da zalunci da almundahana da cin hanci da rashawa, wadanda boyayyun alamu ne na rashin imani da karkacewa daga gaskiya da keta umarnin Allah da watsuwar rashin adalci da sauran miyagun dabi’u kamar shan giya da zinace-zinace da luwadi da madigo da caca da zubar da jini da lalacewar tarbiyya da sauransu, duk wannan al’umma da ka bari a kan gwadabe mai haske ta koma ga wadannan halaye na ‘Jahiliyya.’ Bayan kuwa irin wannan mummunan yanayi da dan Adam ya rayu a baya ne Allah Ya aiko ka a matsayin Manzo da Ya bayyana ka da “Rahama ga talikai.” Domin ka ceto dan Adam daga duhun kafirci da zalunci zuwa ga hasken adalci da imani.