Akwai rahoton da ya nuna an saki wata amarya saboda ta yi wa mijinta abinci amma ta sanya masa nama tsoka biyu maimakon biyar da ta saba sanya masa. Amaryar ta ce ta yi haka ne saboda wadansu bakin da suka yi daga bangaren mijin ba tare da saninsu ba. Don kada ta ji kunya sai ta rage naman da take sanya wa mijin a abinci ta sanya wa bakin. Bayan mijin ya koma gida da bude kwanon abinci ya ga tsokar nama biyu maimakon biyar da ya saba gani ba tare da bincike ko bin bahasi daga amaryar ba, sai ya ce ya sake ta. Wannan abu ya daure wa jama’a da dama kai. Daga baya ne da mijin ya bincika sai ya gane ta fi shi gaskiya, nan ya shiga ’yan kame-kame da niyyar mayar da matarsa amma iyayenta suka ki amincewa har aka raba auren. Sun nuna mijin yana da matsala, don babu tabbacin ba zai sake aikata irin haka a nan gaba ba. A nan wa gari ya waya? Daga nan mijin ya shiga wani yanayi.
Sannan akwai labarin da ya nuna yadda wani mutum ya saki matarsa a kan Naira dari biyu. Yadda abin ya faru shi ne, magidancin ya ba matarsa kudin cefane da niyyar za ta mayar masa da Naira 200 da za su yi rara. Bayan ya fita ne sai matar tasa ta yi baki. A yayin da bakin za su tafi sai ta rasa yadda za ta yi, inda ta yi amfani da canjin Naira 200 ta ba su a matsayin kudin mota. Bayan mijin ya dawo ta yi masa bayani sai ya kekasa kasa ya nuna atafau sai ta biya shi. Nan dai gardama ta sarke a tsakaninsu inda ta kai ya yi mata duka sannan ya hada mata da saki.
Shi kuma wani magidanci kamar yadda wani rahoto ya nuna ya saki matarsa ce saboda ta antaya masa ruwa lokacin da yake kwance. Yadda al’amarin ya faru shi ne, amaryar ta debo ruwa ne a cikin daki za ta nufin dakin dafa abinci don ta yi amfani da shi, amma cikin kuskure sai ta zame inda bokitin ya kwace daga hannunta ta antaya wa mijin ruwa a lokacin da yake kwance a kan katifa. Nan take ya yi firgigit ba tare da neman wani bahasi ba ya ce ya sake ta, wai ta yi haka ne da gangan. Makwabta sun yi kokarin su lallashe shi, amma ya nuna ba zai mayar da ita ba. Daga nan ne wadansu suka yi tunanin watakila yana neman hanyar da zai rabu da ita ce saboda yana son ya kara sabon aure kuma ya rasa yadda zai yi, da tsautsayi ya gitta sai ya yi amfani da wannan dama ya saki matar.
Shi kuwa wani magidanci saboda rashin tausayi da tunani ya saki matarsa ce kamar yadda wani rahoto ya nuna a kan ta yi amfani da silifas dinsa ba tare da izininsa ba. Kodayake ya saya wa matar tasa takalma iri-iri amma yadda ta daukar masa silifas lokacin da ya matsu yana son ya zagaya ban-daki, abin ya yi matukar kona masa rai. Da ya nemi jin dalilin da ya sa ta aikata haka sai ta fara ’yan kame-kame inda nan take ya sake ta.
Ire-iren wadannan matsaloli suna da matukar yawa ba a Jihar Kano kadai ba, har a daukacin jihohin Arewacin kasar nan.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, koda yake an fi dora wa maza laifi a game da yawan sakin aure, a bangaren matan ma suna da nasu laifin.
Insha Allahu a makon gobe za mu tabo wasu abubuwa da mata ke yi da hakan ke sa a sake su ba tare da laifin mazan ba. Fatarmu dai Gwamnatin Jihar Kano ta yi kwakkwaran bincike kafin ta bullo da dokar hana sakin aure a jihar.
Sai mako na gaba
Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805