Yau cikin yardar Allah da kudirarSa an samu kwana biyar a cikin watan azumin Ramadan na bana (Shekarar 1440 Bayan Hijira), wadda ta yi daidai da shekarar 2019, Miladiyya. Fara azumntar watan ya biyo bayan tsayuwar jinjirin watan Ramadan da Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya bayar a ranar Lahadin da ta gabata.
Sanarwar Sarkin Musulmin ta tabbatar da cewa a bana an ga tsayuwar jinjirin watan Ramadan a garuruwan Minna babban birnin Jihar Neja da Dutse babban birnin Jihar Jigawa da Tsafe da ke Jihar Zamfara, don haka ya ce da wannan ya zama wajibi ga dukkan Musulmin kasar nan su fara azumin watan Ramadan daga ranar Litinin da ta gabata, kasancewarta 1 ga watan na Ramadan na bana.
Kasancewar azumin watan Ramadan na cikin shika-shikan Musulunci guda biyar. Allah (SWT) Mai tsarki da Daukaka Shi Ya farlanta azumtar watan Ramadan ga dukkan Musulmi da Musulma, balagai masu cikakken hankali da lafiya a cikin Alkur’aninSa Mai girma a Suratul Bakara aya ta 183, inda Ya ce “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku, za ku yi takawa.” Wannan ayar kadai kamar yadda aka saukar da ita, ta ishi duk wani mai neman ya hadu da Allah cikin kwadayin rahamarSa da jin tsoron azabarSa muddin yana da lafiya, ya dage ya azumci watan na Ramadan.
Ba ma mutum ya himmatu cikin azumtar watan kadai ba, a’a wajibi ne ya himmatu wajen kiyaye dukkan ka’idoji da sharuddan azumin, wadanda suka wuce batun kamewa daga ci da sha da yin jima’i a lokacin da yake dauke da azumin, har da nisantar aikata dukkan wasu miyagun ayyuka, komai kankantarsu da mutum yake gani da yasassarar magana da dama kowane abu da Allah Ya haramta wa bayanSa yi, ko ba a cikin Ramadan ba, balle a lokacin azumi. Watan azumin Ramadan, wata ne da malaman addinin Musulunci bisa ga fahimtarsu ta Alkur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW), suke karantar da mu irin dimbin alheran da ke ciki da Allah Bai tanade su a cikin sauran watanni 11 ba.
Malaman sun bayyana mana cewa goman farko na watan, cike suke da rahama, na tsakiya gafara na karshe kuma ’yantarwa daga wuta. Don haka dan uwa da ’yar uwa Musulmi ko a nan aka tsaya, yaya mutumin da Allah Ya azurta da riskar wannan lokaci mai tarin albarka, kuma yana cikin koshin lafiya zai yi sakaci ko ya shagala ya ki yin ibada a wannan wata mai alfarma?
A cikin wannan wata ne Allah (SWT) Ya saukar da Alkur’aninSa Mai girma, kuma a cikin daren Lailatul Kadari, daren da a wannan watan ake dacewa da shi. Daren da Allah (SWT) Ya ce ya fi wata dubu, ma’ana idan Allah Ya sa mutum ya yi ibada a daren ya kuma dace, to, ibadar ta fi ibadar sama da shekara 83. Tirkashi! Dan uwa ko ’yar uwa, dubi shekara 83, a ce a dare daya ka dace ko kin dace da samun ladar ibadar wannan tsawon lokaci, ai kun san watan ba na wasa ba ne. Allah Ka rabautar da mu.
Sanin wannan falala ta watan azumin Ramadan da neman dacewa da ita, ya sanya idan watan ya tsaya, a kasashen Musulmi kafatan, Musulmin suke kara ninka ayyukan alheran da suke yi, walau ta fannin ciyarwa ko fitar da hakkin Allah a kan dukiyar da Ya ba su, wato fitar da Zakka da yawaitar halartar wuraren da ake tafsirin Alkur’ani Mai girma da yawaita nafilfili, musamman tsayuwar dare da karance-karance don kara fahimtar addini da zuwa aikin Umarah wanda ya fi soyuwa a lokacin watan Ramadan da kuma yawaita dukkan wasu ayyukan alheri da suke fatan dacewa da kara kusantar da su ga rahamar Allah SWT. Malamai na karantar da mu cewa Allah (SWT) Yana cewa: “Azumin watan Ramadan naSa ne, kuma Shi zai saka wa mai azumin.” Bisa ga sirrin da ke cikin yin azumin ya kebanta ne tsakanin bawa da Ubangijinsa, ma’ana mutum na iya shiga daki ya ci ya sha ko kuma ya yi jima’i da rana da ma yin sauran ayyukan da ka iya karya azumi, amma ya fito ya ce wa jama’a yana azumi, wanda sanin haka sai Allah (SWT). Don haka Allah (SWT) Ya ce azumi naSa ne, kuma Shi zai saka wa mai azumi. Allah Ka tsare mu, Ka kuma sa mu dace amin summa amin.
A bisa al’ada, duk lokacin da watan azumi ya karato jama’a kan shiga hidimomin kashe kudi, sabanin sauran lokuta, ko dai a kan tanade-tanaden kayayyakin abinci da abin sha don iyali ko don sadaukarwa ga jama’a. A kan kuma shiga hada-hadar yi wa kai da iyali da ma ’yan uwa sababbin suturu kai har ma takalma don bikin Sallar.
A bana dai Allah cikin ikonSa da rahamarSa, babu labarin hauhawar farashi a kan irin wadannan kayayyakin masarufi, kamar yadda aka saba samu a irin wannan lokaci, sai dai a yi batun tsananin rashin kudi a hannun talakawa da aka dade ana fama da shi a kasar nan.
Alal misali farashin kayayyakin masarufi irin su shinkafa da sukari da man girki a Kasuwar Singa da ke Kano, zuwa wannan lokaci kusan duk suna nan yadda suke kafin shigowar azumin. Buhun shinkafa ’yar kasa yana tsakanin Naira 13,500 zuwa 14, 000, buhun sukari shi ne ya karu da Naira 150, wato daga Naira 13, 200 zuwa Naira 13,350, ita kuwa babbar jarkar mai mai lita 25, sauki ma aka samu a kan farashinta daga Naira 12,000 zuwa Naira 10,700. Haka labarin yake a kan farashin shadda da yadidduka da atamfofi a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano. Da Naira 3,500, za a iya samun turmin atamfa da za a iya daurawa don fitar kunya, akwai ma na kasa da haka amma ta roba ba auduga ba. Farashin shadda da sauran yadidduka irin su Dan Aba duk suna nan yadda aka san su a da. Saura da me? Sai mu yi addu’ar Allah Ya karbi ibadunmu Ya sa mu dace, Ya dora shugabanninmu da mu mabiyansu a kan hanyar daidai, ta yadda kowa zai taka tasa rawar da ta kamata cikin kamanta gaskiya da adalci, ko ma samu fita daga annobar talauci da ta rashin tsaro da tashe-tashen hankula da ke haddasa kashe-kashe da yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sauran miyagun ayyukan ta’addanci da suka game kasa, alfarmar wannan wata, amin summa amin. Mu sha ruwa lafiya.