✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan wasannin da Cutar Kurona ta shafa a Nahiyar Turai

Wasannin gasar La Liga ta Sifaniya da kuma Lig 1 ta Faransa za a buga su ne ba tare da ‘yan kallo ba saboda fargabar…

Wasannin gasar La Liga ta Sifaniya da kuma Lig 1 ta Faransa za a buga su ne ba tare da ‘yan kallo ba saboda fargabar ci gaba da yaduwar Cutar Kurona.

Hukumar La Liga ta ce, hukuncin zai shafi wasannin mako biyu masu zuwa, yayin da ita kuma ta Faransa ta ce an dakatar da ‘yan kallon ne har zuwa akalla 15 ga watan Afrilu.

La Liga, ta ce ta bi shawarar ma’aikatar lafiyar Sifaniya ne. Ita kuma gwamnatin Faransa a ranar ta hana duk wani taron jama’a ta yi, indai suka haura dubu.

Kazalika za a buga wasan Zakarun Turai na Champions League tsakanin Barcelona da Napoli ba tare da ‘yan kallon ba, a ranar 18 ga watan Maris a filin wasan na Camp Nou.

“An dauki matakin ne saboda dalilan lafiya kadai,” in ji Joan Guix, wani mai magana da yawun gwamnatin yankin Catalumya a Sifaniya.

Shi ma wasa tsakanin Brussia Dortmund da Paris St-Germain na Champions League da za a buga gobe Laraba babu ‘yan kallo za a yi shi.

Har wa yau, wasan Manchester United da kungiyar LASK Linz na Europa League da za a buga ranar Alhamis zai kasance babu magoya baya. Za a buga wasan a kasar Australia.

An dakatar da duk wasu harkokin wasanni a Italiya har zuwa akalla 3 ga watan Afrilu saboda Cutar Kurona. Dakatarwar ta kunshi wasannin gasar Serie ‘A’, amma ban da tawagar kasar da kuma kulob da suke buga wasannin kasa da kasa.