✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan mutane na boye ’yan mata a Kasuwar Gujungu

Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta koka kan abin da ta kira cewa wadansu manyan mutane suna kama wa kananan yara mata dakuna suna lalata…

Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta koka kan abin da ta kira cewa wadansu manyan mutane suna kama wa kananan yara mata dakuna suna lalata da su a kasuwar Gujungu da ke jihar.

Kwamandan Hisba ta Jihar Jigawa, Malam Aminu Baba Waziri wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce yanzu kasuwar ta Gujungu tana neman zama maboya da manyan mutane suke amfani da ita wajen lalata kananan yara mata da suke daukowa daga jihohin Yobe da Bauchi da Kano da Jigawa suna kama masu dakuna suna lalata da su.

Malam Aminu ya nuna takaicinsa a kan yadda manyan banzan suke dauko kananan yara masu karancin shekaru suna kama masu dakuna suna ajiye su a matsayin dadiro suna aikata fasadi da su a kasuwar.

Ya ce a baya sun samu bayanin cewa kasuwar ta zama maboya ta karuwai da ’yan bori da makada, amma yanzu lamarin ya bunkasa inda batagari suke neman mayar da kasuwar maboya masu aikata laifi.

Kwamandan ya ce maganar kade-kade da casu kuwa wannan ba sabon al’amari ba ne a kasuwar ta Gujungu, kuma suna da rahoton cewa kwaya da tabar wiwi da giya a gidajan karuwai lamarine da ba a boyewa a kasuwar, wadda ta zama kamar bakin ruwa da ’yan yawon shakatawa suke baje koli.

Ya ce sun sa jami’an tsaron farin kaya suna tattara musu bayanai kan ayyukan batagarin da ke kasuwar da sauran kasuwannin jihar domin kawo karshen lamarin.

Malam Aminu ya ce sun tura jami’ansu na farin kaya zuwa kananan hukumomin Jahun da Gagarawa da Taura domin taimaka wa Hukumar Hisba da bayanan sirri don gano maboyar batagari da suke kasuwanni. Ya ce sun dauki matakin haka ne saboda yawan korafe-korafen da suke samu daga mutane da ke cin kasuwar da masu makwabtaka da wuraren da ake aikata masha’a.

Kwamandan ya nuna damuwa kan yadda wadansu matasa suka kai wa ’yan Hisba hari a Karamar Hukumar Garki dauke da miyagun makamai saboda sun hana su yin rawar D.J a garin da kewaye.

Ya ce sun samu nasarar kama mutum 13 daga cikin wadanda ake zargin kuma za su gabatar da su gaban kotu domin a yi musu hukunci.