Mazauna yankunan Bida, Gbako da Katcha a Jihar Neja sun koka kan yadda suka ce manyan motocin da ke bin babbar hanyar Bida zuwa Minna na barazana ga rayukansu.
Sun roki Gwamnatin Tarayya da ta kawo musu dauki ta hanyar dakatar da motocin daga bin hanyar.
- Barazanar direbobi za ta kawo karancin mai a arewacin Najeriya
- Zanga-zangar karin kudin mai da wuta na nan tafe – NLC
Sakataren Kungiyar Masu Ruwa da Tsaki na Jam’iyyar APC, Reshen Mazabar Dan Majalisar Rarayya ta Bida/Gbako/Katcha, Yahaya Mustapha, wanda ya yi kiran a madadin al’ummar yankin ya kuma roki gwamnatin ta gaggauta rufe hanyar cikin kwanaki biyar.
A cewarsa, yawan zirga-zirgar manyan motocin a hanyar ya taimaka matuka wajen kara lalacewarta da kuma mayar da ita tarkon mutuwa gare su da sauran masu amfani da ita.
Ya ce, “Mun samu sa’ida sosai lokacin da Gwamnatin Jihar Neja ta yanke shawarar rufe hanyar ga manyan motoci, muna ganin matakin ya dace saboda zai taimaka wajen saukaka gyaran hanyar ba tare da wani tarnaki ba.
“Amma abin takaici da Allah-wadai sai sai Gwamnatin Tarayya ta matsa wa jihar lamba dole sai da aka sake bude hanyar.
“To amma muna sa ran gwamnatin za ta kara azama wajen kammala aikin da kuma tabbatar da cewa ya dangana har da hanyar Lambata zuwa Lapai zuwa Bida.