✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan motoci 40 za su kwaso ’yan Najeriya daga Sudan zuwa Masar —Gwamnatin Tarayya

An biya kowacce mota dala 30,000.

Gwamnatin Tarayya ta ce manyan motoci 40 aka tanadar domin kwaso ’yan kasar da suka makale a Sudan, don kai su Masar inda za a dauko su a jiragen sama zuwa Najeriya.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Jin-kai, kuma shugaban cibiyar da ke sa ido kan halin da ’yan kasar ke ciki a Sudan, Dokta Nasir Sani Gwarzo ne ya bayyana haka jim kadan bayan wata ganawar sirri da manyan jami’an ma’aikatar a Abuja.

Ya ce an samar da manyan motocin daukar fasinja 40, domin aikin kwasar ’yar kasar da suka makale a Sudan din, kuma an biya kowacce mota dala 30,000.

Ya ce jinkirin da aka samu a kan iyakar kasar Masar, an same shi sakamakon rashin biyan kudin da babban bankin kasar ya yi a kan lokaci, tare da bukatar biyan kudin bisa da gwamnatin Masar ta yi.

Dakta Nasir Gwarzo ya ce, masu motocin sun bukaci a biya su kudinsu gaba-daya, duk kuwa da suna sane da cewa ba zai yiwu a tura kudi kai tsaye zuwa Sudan ba, dole sai da wakilai.

Ya kara da cewa ma’aikatar na aiki ne da Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da Hukumar da ke Tattara Bayanan Sirri a kan Laifukan da suka shafi kudi ta NFIU wajen biyan kudaden.

BBC