✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan kasashe biyar da ba za su je gasar kofin duniya ba

A ci gaba da wasannin sharar fage domin neman gurbin buga gasar cin kofin duniya na badi da zai wakana a kasar Rasha, akwai abubuwa…

A ci gaba da wasannin sharar fage domin neman gurbin buga gasar cin kofin duniya na badi da zai wakana a kasar Rasha, akwai abubuwa ban mamaki da dama. A daidai lokacin da wasu ke ganin wasu kananan kasashe da ba su yi fice a harkar kwallon kafa ba sun samu nasarar shiga gasar, sai ga abin mamaki, inda wasu manyan kasashe ba za su samu shiga gasar ba saboda sun gaza samun gurbi a sharar fagen.

Aminiya ta rairayo manyan kasashe guda biyar da izuwa yanzu aka tabbatar ba za su shiga gasar ba. Wadannan kasashen su ne:

1.     Kasar Amurka

2.     Kasar Chile

3.     Kasar Holland

4.     Kasar Kamaru

5.     Kasar Ghana