Akwai wasu fitattun jarumai a masana’antar shirya fina-finai ta Kudancin Najeriya (Nollywood) da suka fito daga gidajen sarauta.
Duk da haka suna gudanar da rayuwarsu kamar yadda sauran gama-garin ke yi, wanda hakan ya sanya mutane shakkun kan asalinsu.
- Da na ga dama da an cafke Peter Obi a Kaduna —El-Rufai
- PDP ta yi Allah wadai da harin da kai wa Atiku a Kaduna
Aminiya ta tattaro wasu fitattun jaruman Najeriya biyar wadanda mutane ba su taba sanin cewa daga gidan sarauta suka fito ba.
1. Rita Dominic: Fitacciyar jarumar Nollywood ce da ke auren dan jarida, Fidelis Asonike. Mahaifinta basarake ne a masarautar Waturuocha da ke karamar hukumar Aboh Mbais a Jihar Imo.
2. Jide Kosoko: Jide ya yi shuhura a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, ya fito ne daga gidan iyalan sarautar da ke Jihar Legas.
Jide Kosoko ya fito a fina-finai masu yawa da suka hada da na Turanci da Yarbanci. Ya auri mata guda biyu Karimat da Henrietta, sai dai Henrietta ta rasu a 2016.
3. Omawumi Megbele: Jaruma ce kuma fitacciyar mawakiya wadda ta taba shiga gasar gwada bajintar da aka yi a Yammacin Afirka. Mahaifinta na rike da masarautar Itsekiri da ke Jihar Delta.
4. King Sunny Ade: Ade ya yi shura a bangaren kidan Juju, wanda hakan ne ya sa aka taba masa sarautar ‘Omoba’ a Kasar Yarbawa.
Mahaifiyarsa ta fito daga gidan sarautar Adesida da ke garin Akure, Jihar Ondo, mahaifinsa kuma basarake ne daga Fadar Masarautar Ondo.
5. Adekunle Gold: Jarumi kuma mawaki, ya auri abokiyar aikinsa, Simi Ogunleye. Shi ma ya fito daga Masarautar Kosoko da ke tsibirin Legas.