✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan Gobe barka da warhaka 00

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku ‘labarin zaki da bawa’. Labarin ya kunshi yadda Manyan gobe za su kasance…

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku ‘labarin zaki da bawa’. Labarin ya kunshi yadda Manyan gobe za su kasance masu taimako a wurin da ake bukatar taimakonsu.
A sha karatu lafiya.

Labarin Zaki da Bawa

An yi wani azzalumin sarki a wani kauye. Wannan sarkin kullum yana kan kuntata wa bayinsa, ga shi ba ya ba su abinci kamar yadda ya kamata. Abin ya ishe su, kuma ba su san yadda za su yi ba.
Rannan sai daya daga cikin bayin ya gudu daji. Ya shiga cikin kogon zaki. Yana cikin hutawa ke nan sai ya ji wata kara kamar ta zaki. Waigawar da ya yi sai ya ga katon zaki cikin jini, bayan ya duba ne sai ya ga wani karfe ya shiga masa kafa.
Nan take ya taimaka wa zakin ta hanyar cire masa karfen, daga nan suka zama abokai.
Da sarki bai ga bawansa ba sai ya sa aka shiga nemansa, har aka kama shi. Sarki ya ce zai masa mummunan horo saboda ya zama izna ga sauran bayin.
Daga nan Sarki ya sa aka tara mutanen kauyensa, sannan aka jefa wannan bawan cikin wani fili da aka zagaye da itatuwa, sai aka sako masa zaki.
Mutanen kauyen suka zuba ido don ganin abin da zai faru, amma ga mamakinsu sai suka ga zaki ya fara lashe bawan sarki. Ashe zakin da bawan ya taimakawa ne. Abin ya ba sarkin mamaki, sai ya hakura da hukuncin kisa da ya yanke wa bawansa, daga karshe aka sake shi
Da fatan Manyan gobe za su kasance masu taimako, kuma su dauki darasi daga wannan labarin.