Gwamnatin tarayya ta gabatar da kimanin Naira biliyan 737 don aiwatar da manyan ayyuka 71 a ma’aikatu bakwai.
Wani bincike da Aminiya ta gudanar kan kasafin kudin shekarar 2018 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ga majalisa makon da ya gabata ya nuna manyan ayyukan da idan aka gudanar da su za su lakume kashi 30 daga cikin dari na Naira tiriliyan biyu da digo 43 da aka ware na manyan ayyuka a shekarar 2018.
Ma’aikatun da za su amfana sun hada da ma’aikatar wutar lantarki da gidaje da Ayyuka da ma’aikatar lafiya da ma’aikatar ilimi da ta Neja Delta da ma’aikatar sufuri da kuma ma’aikatar noma.