Manyan kasar nan sun la’anci wata waka da aka yi don nuna kyama ga kabilar Ibo, wacce a ’yan kwanakin nan take ta yawo a kafofin sadarwar zamani, musamman shafukan sada zumunta.
Wakar wacce a ciki ake jin muryar wata mawakiya da ba a tantance kowace ce ba, tana kalubalantar kabilar Igbo tare da kalaman zage-zage, an tsara ta ce cikin harshen Hausa hade da kida da ’yan amshi.
Shugabanni daban-daban da suka fito daga sassan kasar nan sun yi Allah wadai da wakar inda suka bukaci a binciko mawakiyar da masu hannu a ciki don hukunta su.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ne ya fara Allah wadai da wakar, sannan ya kwatanta ta da irin wadda aka taba yi a kasar Rwanda, wadda ya ce ta haddasa mummunan rikicin kabilanci a kasar. Sai ya yi kira ga jami’an tsaro su gano mawakiyar domin hukunta ta.
Shi ma tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya ce: “Na shiga damuwa lokacin da na ji labarin wata waka da ke nuna kiyayya ga wasu al’ummar Najeriya. Kasancewar irin wannan waka ce ta jefa kasar Rwanda cikin rikici, bai kamata mu dauki batun wakar nan da sauki ba. Don haka ina kira ga jami’an tsaro su yi bakin kokarinsu wajen dakile ta.”
Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa Cif John Oyegun ma ya la’anci wakar inda ya nemi a zakulo wadanda suka yi ta domin hukunta su.
Da yake magana kan wakar, Ministan Watsa Labarai, Alhaji Lai Mohammed ya ce Gwamnatin Tarayya za ta dauki kwakkwaran matakin ladabtarwa da hukunta dukan wadansu mutane da ke yada kalaman kyama da nuna kiyayya ga wasu jama’a a kasar nan. Ya ce, gwamnati za ta yi amfani da hukumomin tsaro da Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabjin ta Kasa (NBC), domin cimma wannan kudiri.
“Gwamnati ba kawai tana duba batun wakar nuna kyama daga Arewa ba ne, tana yin Allah wadai da kowace irin waka irin wannan daga kowane sashi ta fito a kasar nan. Domin haka idan aka samu kowace irin waka da ke nuna kyama ko kiyayya ga wasu jama’a, za a hukunta duk mai yin ta da mai yada ta daga ko’ina yake a cikin kasar nan,” inji Minista Lai.
Shi ma tsohon Gwamnan Jihar Abiya, Cif Orji Uzor Kalu, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta tashi tsaye wajen yaki da irin wadannan wakoki da sauran mutane da ke yada irin wadannan kalamai na batanci ko nuna kiyayya ga wasu jama’a.
Babban Daraktan Hukumar NBC, Dokta Modibbo Kawu, ya sha alwashin hukunta duk wata kafar watsa labarai da aka samu tana yada wannan waka ko makamanciyarta ta kafar sadarwarta. “Wannan waka ta nuna kiyayya al’amari ne mai hadarin gaske, jami’anmu masu bin sawu sun fara aikin tantance kafafen sadarwa da tashoshin watsa labarai na kasar nan, domin gano masu yada wannan waka da nufin hukunta su,” inji Modibbo.
Baya ga manyan mutane kungiyoyi da dama ma sun bukaci a gano wadanda suka yi wakar tare da hukunta su, kuma sun la’anci kalaman batanci da ake samu a kasar nan a baya-bayan nan.