✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manuniya kan azumin nafila bayan na Ramadan (4)

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna…

Da sunan Allah, Mai rahma, Mai jinkai. Lallai dukkan godiya da yabo na Allah ne. Muna gode maSa, kuma muna neman taimakonSa da gafararSa, muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu.  Lallai wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Allah Ya batar, babu mai shiryar da shi.  Ina shaidawa babu abin bauta wa bisa cancanta, sai Allah, Shi kadai, ba Ya da abokin tarayya, kuma ina shaidawa Annabi Muhammadu bawanSa ne, ManzonSa ne (SAW).
Allah Ya dada tsira da aminci ga ManzonSa da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsu har zuwa Ranar karshe.
Bayan haka, mun kwana a mas’ala ta biyu mai cewa: ‘Mai tadawwu’i mamallakin kansa ne,’ a karkashin mas’alolin azumin tadawwu’i, inda muka gabatar da Hadisin Ummu Hani, (Allah Ya yarda da ita), wanda aka ce mai rauni ne, amma an samu shaidar da ta karfafa Hadisin. To, yau ga ci gaba:
Abu Malik Kamal (Sahih Fikhus Sunna…), ya ce, “Na ce, ‘Wannan Hadisi (na Ummu Hani) mai rauni ne, sai dai ma’anar Hadisin Abu Juhaifah (Allah Ya yarda da shi), yana iya zama shaida a kan karfin wannan hujja ta malaman nan biyu (Imam Shafi’i da Imam Ahmad bin Hambal) dangane da wannan magana ta mai azumin tadawwu’i ya yi yadda ya ga dama…”
Hadisin shi ne Abu Juhaifah (Allah Ya yarda da shi), ya ce, “Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya sanya ’yan uwantaka a tsakanin Salman da Abu Darda’i (Allah Ya yarda da su)… (Hadisi ne dogo, amma za a nuna madogarar kawo shi ne kawai a nan)…. Saboda haka sai (Salman) ya shirya abinci ya ce masa (Abu Darda’i) ya ci, shi kuma ya ce, ‘Ni ina azumi.’ Sai Salman ya ce, ‘Ni kuma ba zan ci ba, har sai ka ci.’ Saboda haka sai ya ci…. Sai Salman ya ce masa, “Lallai (ka sani) Ubangijinka Yana da hakki a kanka; ranka yana da hakki a kanka; kuma iyalinka suna da hakki a kanka. Saboda haka ka ba kowane mai hakki, hakkinsa.” Shi ke nan (wanshegari) sai Abu Darda’i (Allah Ya yarda da shi), ya je wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ambata masa abin da ya auku a tsakaninsa da Salman, sai Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Salman ya yi gaskiya.” Sahihin Hadisi ne da Buhari ya fitar a Hadisi na 1,968.
A cikin wannan Hadisi akwai manuniya cewa Abu Darda’i (Allah Ya yarda da shi), ya ci abinci alhali yana azumi kuma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), bai umurce shi da ramawa ba.
Haka nan abin yake karfafa waccan magana ta mai tadawwu’i mamallakin kansa ne shi ne Hadisin A’isha (Allah Ya yarda da ita), inda ta ce, “Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam), wata rana ya ce min, ‘Ya A’isha, ko kuna da wani abinci?’ Sai na ce masa, ‘Ya Ma’aikin Allah, babu wani abinci a wurinmu.’ Sai ya ce, “To, ina azumi ke nan.” Daga nan sai ya fita, sai kuma aka kawo mana wani abinci, ko kuma wani mai ziyara ya ziyarce mu (ya zo da wata hadaya). Yayin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya komo cikin gida, sai na ce masa, ‘An kawo mana wata hadaya, kuma lallai na tanada maka wani abu daga ciki.’ Sai ya ce, “Mene ne?” Sai na ce, “Haisu’ ne (wani irin abinci ne a Madina da ake yi da dabino da kakidi da wani nau’in alkama).” Sai ya ce, “Kawo min shi.” Sai na kawo masa, sai ya ci, sannan ya ce, “Lallai na kasance na wayi gari ina mai azumi.” Sahihin Hadisi ne da Muslim ya fitar a Hadisi na 1,154.
Wannan nassi ne da yake nuna halaccin cin abinci bayan an tabbatar da faruwar azumi. Wannan irin magana kuwa ta tabbata daga Abdullahi dan Abbas da Abdullahi dan Mas’ud da Jabir dan Abdullahi da isnadojin hadisai sahihai, kamar yadda ya zo a littafin Musannafu Abdurrazzak (7,767-7,768; 7,771); da Sunan Albaihaki, mujalladi na 4, Hadisi na 277.
Su kuwa Imam Abu Hanifa da Malik (Allah Ya yi masu rahama), sun tafi a kan cewa wanda duk ya wayi gari yana tadawwu’i, ya karya da gangan, to, sai ya rama shi, kamar yadda bayani ya zo a cikin littafin Sharh Ma’ani Al’asar, mujalladi na 2, shafi na 111 da Almudawwana, mujalladi na 1, shafi na 183.
Sun kafa hujjar haka ne saboda abin da aka ruwaito daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce mata da Hafsa (Allah Ya yarda da su), a lokacin da suka kasance suna azumi, sai suka karya: “Ku rama wata rana ta daban maimakonsa.” Hadisin mai rauni (da’ifi) ne da Tirmizi, Hadisi na 735; da Annasa’i, a cikin littafin Alkubra, Hadisi na 3,291 da Ahmad, mujalladi na 6, Hadisi na 263 suka fitar.
Sannan sun yi hujja da wani karin ruwaya da aka samu a Hadisin A’isha (Allah Ya yarda da ita), a cikin cin abincin da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yi bayan yana azumi, sai ya ce, “Lallai ni na yi nufin azumi, sai dai zan azumci wata ranar a madadin wannan.” Ruwaya ce ‘shazi’ (tilo da ba ta da karfin hujja), wadda Annasa’i, a cikin littafin Alkubra, Hadisi na 3,300 da Abdurrazzak, Hadisi na 7,793; da Dar-kudni, mujalladi na 2, Hadisi 177 da Baihaki, mujalladi na 4, Hadisi na 275 suka fitar.  Annasa’i ya ce, “Wannan kuskure ne.” Baihaki ya ce, “Wannan, a wurin ma’abuta Ilimin Hadisi, ba abin kiyayewa ba ne.”
Sannan sun yi kiyasi da hukuncin cika azumin tadawwu’i da hukuncin cika Hajji da Umara, kuma wannan kiyasi ne wanda yake tare da rarrabewa domin wanda ya lalata sallarsa ko azuminsa, sai a ce masa mai sabo, idan ya zarce da yin sallar ko azumin alhalin sun baci. Amma mai aikin Hajji, shi ana ma umurtarsa ne da ya cika shi a bataccensa, bai halatta gare shi ya fita daga aikin ba, har sai ya cika shi a bacen, sannan kuma ya rama shi. Ka ga kuwa lamarin ba haka yake ba ga mai Sallah ko azumi, saboda haka wannan kiyasi a kan Hajji, bai kiyasantu ba. Haka nan, shi wannan kiyasi a nan, kiyasi ne da ya yi takara da nassi, saboda haka ba ma za a yi dubi da shi ba. (Sahih Fikhus Sunnah, Juz’i na 2, shafi na 126).
3. Shin ana iya tadawwu’i alhali ga ramuwar Ramadan?:  
Mazhabar jamhurun Salaf da wadanda suka maye gurbinsu (Khalaf) sun tafi a kan halaccin jinkirta ramuwar Ramadan – ga wanda ya sha azumin saboda lalura – halacci yanke, babu wata tantama game da haka. Sannan ba wani sharadi da ya nuna a yi gaggawar ramuwar ko da kuwa da kasancewar damar yin hakan tun farko.
Inda suka yi sabani shi ne yiwuwar azumin tadawwu’i alhalin ga ramuwar Ramadan a kan mutum.  Za mu ga wannan sabani da kuma mafitarsa ko akasi, idan Allah Ya nufe mu da kaiwa mako na gaba.  Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!