✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mansurah Isah ta yi sabon aure

An ɗaura auren Mansura a yammacin wannan Alhamis ɗin.

Tsohuwar jarumar Kannywood kuma tsohuwar matar jarumi Sani Musa Danja, Mansurah Isah ta amarce cikin daren nan.

Aminiyarta Samira Ahmad ce ta bayyana haka cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram.

Samira ta wallafa ce: “Alhamdulillah, an daura auren Mansurah Isah yanzu. Allah Ya sanya alheri Ya ba su zaman lafiya. Amin.”

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Mansurah Isah ta kura bayan ta sanar da cewa ba ta shirin komawa gidan tsohon mijinta, Sani Danja.

Mansurah ta ce sam ba ta kewar komawa gidan Sani Danja, ballanta maganar shirin komawa gidan.

Jarumar ta yi wannan furuci ne ne a yayin wata tattaunawa da Kafar DW, wacce ta karade shafukan sada zumunta a wannan mako da muke ciki.

Ta sanar da haka ne lokacin da dan jaridar da suke tattaunawa ya tambaye ta ko tana shirin komawa gidan tsohon mijin nata.

Cikin raha jarumar ta kada baki ta gargadi dan jaridar da ya fita a idonta, ta rufe kuma a yanzu “ba na shirin komawa gidansa.”

Mutane da dama dai na ganin maganganu na Mansura ba su kai zuci ba, kuma har yanzu da alamar tana son komawa ne gidan tsohon mijin nata.

Kwatsam kuma sai ga labarin ta sake wani auren.