Wata Kotun Majistare da ke Makurdi a Jihar Binuwai ta tura wani manomi mazaunin kauyen Tombo a Karamar Hukumar Buruku gidan yari, bisa zargin hada baki wajen lakada wa wani dan acaba duka wanda ya yi ajalinsa har lahira.
Ana zargin shi da hada baki da wasu mutum uku ne domin yi wa dan acaban mai shekara 32, Fanen Vanger dukan da ya sa ya mutu.
- Kotu ta raba auren shekara 10 saboda rashin abinci
- NDLEA na son a fara yi wa masu yi wa kasa hidima gwajin miyagun kwayoyi
Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa wani dan uwan marigayi Aondohemba Vanger ne, ya kai rahoton lamarin ofishin ’yan sanda na Buruku a ranar 20 ga watan Afrilu, cewa kaninsa ya fita yin sana’ar acaba kamar kullum amma bai dawo gida ba.
Ya ce wanda ya shigar da karar ya kara da cewa daga baya ya samu labarin cewa gungun wasu mutanen kauyen Tombo sun kashe dan uwansa ta hanyar yi mishi dukan tsiya.
Ya kuma ce wadanda ake zargin sun jefa gawar dan acaban a cikin kogin Buruku.
Mai gabatar da kara ya ce tun da farko ’yan sanda sun cafke manomin da wasu tare da gurfanar da su a gaban kotun.
Tuni alkalin kotun ya tisa keyarsu zuwa gidan dan-kande, sannan ya dage sauraren shari’ar.