Wasu manoma a yankin garin Chilo da ke Karamar Hukumar Akko ta Jihar Gombe, sun koka kan yadda makiyaya ke kada dabbobinsu cikin dare suna cinye musu gonaki.
Manoman sun ce sun kama shanun makiyayan inda suka mika wa kwamitin da gwamnati ta kafa kan hana makiyaya shiga gonakin al’umma.
- Kungiyar ma’aikatan Majalisar Gombe ta janye yajin aiki
- Damar tserewa daga Najeriya nake jira —Buhari
Manoman sun ce da hadin kan ‘yan banga suka samu nasarar kama makiyayan tare da shanunsu suka mika su ga kwamitin a Karamar Hukumar Yamaltu Deba.
Sai dai manoman sun ce suna zargin wasu daga cikin ‘yan kwamitin da sakin shanun, lamarin da ya sanya suke bukatar gwamnati ta kawo musu dauki.
Wani manomi mai suna Malam Bello, ya bayyana wa Aminiya cewa cikin dare makiyayan suka bi suka cinye musu gonaki da suka shafe tsawon watanni hudu suna nomawa.
Shi ma Dahiru Inusa, cewa ya yi suna neman alfarmar gwamnati da masu ruwa da tsaki su bi musu kadin amfanin gonakinsu da makiyayan suka lakwume dare daya.
“Bayan mun kama shanun mun mika wa ’yan kwamiti sai su kuma suka saki shanun.
“Mun samu labarin cewa kwamitin da gwamnatin ta kafa sun mayarwa da Fulanin shanunsu ne bayan mika musu da suka yi don daukar mataki.
“Hakan zai iya bai wa Fulanin damar sake dawowa su cinye sauran abin da ya rage a gonakin.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin ’yan kwamitin ko Shugaban Karamar Hukumar Yamaltu Deba, amma lamarin ya ci tura.
Sai dai wata majiya a Karamar Hukumar da ta bukaci a sakaya sunanta, ta shaida cewa ’yan kwamitin sun mayar wa makiyayan shanun ne saboda nauyin dawainiyar ciyar da su.