✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma dubu 36 za su ci gajiyar shirin noman Fadama na GO-CARES a Gombe

Cikin manoma dubu 36 da 300 da za su amfana dubu 31 manoma ne da aka ba su kayan amfanin gona.

Akalla manoma dubu 36 ne a Jihar Gombe za su ci gajiyar shirin noman Fadama na GO-CARES karo na uku da Ma’aikatar Aikin Gona da Kiwon Dabbobi ta shirya ta ba da iri don noman rani da maganin feshi da sauransu.

Ko’odinatan Shirin a Gombe Dokta Babayo Makka ne ya sanar da hakan a lokacin kaddamar da rabon kayan wa Manoma a harabar Ma’aikatar ta aikin Gona.

Dokta Makka, ya yaba wa Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, kan ba da kudi a kan lokaci don faranta wa manoma inda ya ce hakan ya tabbatar da cewa Gwamnan yana kokari.

A cewarsa, cikin manoma dubu 36 da 300 da za su amfana dubu 31 manoma ne da aka ba su kayan amfanin gona irin masara da magungunan feshi da na shuka da takin zamani da kuma dabbobi da sauran abubuwan more rayuwa.

Sauran manoman da ba su da galihu su dubu 2,800 da suka hada da mata da matasa su kuma an tallafa musu da injunan ban- ruwa da injin markade don ganin yadda za su taimaki kansu.

A cewar Ko’odinatan za su gina lambatu 4, za su gyara kananan dam-dam 8 don shayar da dabbobi a karkashin Shirin Noman Fadama da zai samar da aikin yi kai-tsaye ga mutum dubu 2,500.

Wasu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin da suka zanta da wakilinmu sun ce suna cike da farin cikin za su yi amfani da abubuwan da suka samu don farfadowa daga halin da aka tsinci kai na cutar Kwarona Idan za a iya tunawa manoma daban-daban maza da mata a jihar suka amfana da kashi na farko da na biyu na shirin, inda aka ba su kayayyakin aikin gona da irin shuka da magunguna