Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da mutuwar wani mutum, yayin da fiye da 30 suka nutse bayan da wani kwale-kwale ya kife a kogin Dundaye da ke ƙaramar hukumar Wamakko a Jihar Sakkwato.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi, lokacin da mutanen ke hanyar zuwa gonakinsu.
Shugaban hukumar mai lura da jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara, Aliyu Shehu-Kafin Dangi, ya tabbatar da faruwar hatsarin.
Amma ya ce jami’an hukumar sun fara aikin ceto mutanen da hatsarin kwale-kwalen ya rutsa da su.
“Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na safe, kuma mun zo da jami’anmu domin a sanin yadda za a ceto mutanen da suka nutse,” in ji shi.
Direban kwale-kwalen, wanda shi kaɗai ne da ya tsira, ya shaida cewa suna kan hanyarsu ne daga garin Dundaye zuwa Fadama domin aikin shinkafa lokacin da lamarin ya faru.
Hatsarin jirgin ruwa dai ba baƙon abu ba ne a Najeriya, inda lamarin ya fi ƙamari a yankunan Kebbi, Sakkwato da kuma Jihar Zamfara.